Babu maganar wahalar man fetur, kungiyar NUPENG ta fasa tafiya yajin-aiki a yau

Babu maganar wahalar man fetur, kungiyar NUPENG ta fasa tafiya yajin-aiki a yau

  • Kungiyar NUPENG ba za ta soma yajin-aikin da tayi niyya a fadin kasa a yau ba
  • Wani jagoran kungiyar, Tayo Aboyeji ne ya bada sanarwar dakatar da shiga yajin
  • Direbobin motocin mai sun dauki wannan matsaya domin a zauna da gwamanti

Lagos - A ranar Lahadi, 10 ga watan Oktoba, 2021, kungiyar NUPENG ta ma’aikatan mai da gas na kasa, suka bada sanarwar dakatar da shiga yajin-aiki a yau.

Daily Trust tace kungiyar direbobin tankokin mai na PTF da ke karkashin NUPENG, ta janye yajin-aiki a sakamkon tattauna wa da gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar NUPENG na reshen Kudu maso yamma, Tayo Aboyeji ya shaida wa hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, cewa sun fasa yin yajin-aikin.

Da yake hira da manema labarai a Legas, Mista Tayo Aboyeji yace sun dauki wannan mataki ne domin su iya kammala zama da wakilan gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon APC yace ‘Yan Najeriya su shiryawa bakar wahala bayan ganin kasafin 2022

Aboyeji ya bayyana cewa suna sa rai gwamnatin Najeriya ta duba korafinsu, ta kuma magance mata su. Hakan zai sa ayi watsi da batun tafiya yajin-aikin.

Motocin man fetur
Motocin dakon mai Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bayan wani gajeren zama da wakilan gwamnati, shugabannin kungiyar (NUPENG) sun dauki matakin dakatar da yajin-aiki saboda kishin-kasa.”
“Za mu cigaba da zama da gwamnati a cikin mako, da nufin za a shawo kan koken kungiyar.” - Tayo Aboyeji

Meyasa NUPENG take barazanar janye aiki?

Kungiyar ta NUPENG tana kukan cewa ana fama da matsalar kyawun tituna a Najeriya, wanda hakan ya jawo asarar dukiya da mutuwar direbobi a hanyoyi.

“Ba wannan ne karon farko da muka bayyana shirin shiga yajin-aiki, sai mu dawo mu janye ba, domin hakan ya shafi mafi yawan al’ummar Najeriya.” - Ini Aboyeji

Rahoton yace kafin nan an ji Mai magana da yawun bakin NNPC, Garba Deen Mohammed yana rokon NUPENG ta hakura da zuwa yajin-aiki a wannan yanayi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

Motoci za su ci N1.6bn a kasafin 2020

Dazu kun ji cewa a kasafin da aka yi na shekara mai zuwa, kudin da za a kashe na saye da kuma gyaran motocin fadar Shugaban kasa ya zarce Naira biliyan 1.5.

Haka zalika gwamnatin tarayya ta na sa ran batar da N650m a kan aikin mambilla a shekara mai zuwa. Kwangiar ya ci Naira biliyan 10 a cikin shekaru goma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel