Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

  • Masana sun gargadi 'yan Najeriya kan tsadar farashin iskar gas da ke addabar mutanen kasar
  • Masana sun ce, akwai yiyuwar farashin ya ci gaba da cillawa sama matukar ba a yi wani abu ba
  • A halin yanzu, 'yan Najeriya da dama na kokawa kan yadda farashin sikar gas yake kara hauhawa

Jaridar Punch ta ruwatio cewa, masana sun gargadi 'yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za su fara siyan iskar gas a kan farashi mai tsananin tsada. Wannan kenan a cewar 'Yan kasuwa na Iskar Gas.

'Yan kasuwar sun nuna damuwar su kan karancin shigo da gas da ke haifar da hauhawar farashinsa.

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan
Yadda tsadar gas ya tunkaro Najeriya | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, 'yan kasuwan sun yi gargadin cewa iskar gas mai nauyin kilo 12.5 da a halin yanzu ake sayar dashi sakanin N7,500 zuwa N8,000 na iya tashi zuwa N10,000 kafin watan Disamba idan ba a yi wani abu don magance tsadar ba.

Kara karanta wannan

Buhari: Mu na da sabbin makaman yakar kowanne irin rashin tsaro

'Yan kasuwar sun koka da yadda 'yan Najeriya da yawa suka koma amfani da itace, gawayi, garin katako, da sauran hanyoyin makamashi marasa inganci wanda farashin su ma ya fara tashi.

Babban sakataren kungiyar ‘yan kasuwar ta kasa LPG, Mista Bassey Essien, shine ya bayyana hakan yayin tattaunawar da wani babban dandalin Platforms Africa ya shirya.

Platforms Africa wani dandamalin yanar gizo ne na masu ilimi, ginshikan manufofi da jagororin ra'ayi a nahiyar Afrika..

Essien ya ci gaba da cewa akwai bukatar gwamnati ta yi bitar cajin shigo da kayayyaki da aka shigo da su kwanan nan da kuma harajin VAT, in ba haka ba “farashin iskar gas na iya kaiwa N10,000 kan silinda mai nauyin kilo 12.5.”

Ya ce:

“Yau (Asabar), farashin ya tashi zuwa N7,500 da N8,000. Farashin iskar gas shine tsoron mu da abin da muke kokarin gujewa.

Kara karanta wannan

Bayan sa'o'i 4, layukan MTN sun dawo aiki, yan Najeriya sun yi korafi

"A farkon shekarar nan ana sayar tan 20 na iskar gas a kasa da N5m amma a yau, ana sayar da tan din akan N10.2m. Muddin akwai wannan karancin shigowar, adadin da ake samu da kuma karfin bukata zai ci gaba da kara farashi zuwa sama.”

Gwamnatin Buhari ta magantu kan yunkurin hana shigo da tukunyar gas Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta da wani shiri na nan take don hana shigowa da tunkwanen gas a wani bangare na fadadawa da aiwatar da harkar a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Dayo Adesina, babban mataimaki na musamman kan harkar iskar gas a ofishin Mataimakin Shugaban kasa, ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce gwamnati na aiki kan fara gina na ta na cikin gida kafin ta yi tunanin hana shigowa da gas din kwata-kwata.

Kara karanta wannan

Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

A cewar Adesina, wanda kuma shi ne Manajan Shirye-shirye na fadadawa da aiwatar da LPG na kasa, har yanzu Najeriya na da gibin tukwane da yawa da za ta cike yayin ganawa a shirin fadada LPG.

Ya bayyana cewa shirin shine a samar da LPG zuwa kauyukan da ke nesa da kuma hana amfani da itacen girki da sauran man da ke da illa ga muhalli.

Bincike: Gida mai yawan mutum 4 na bukatar kashe N10k don dafa shinkafa jollof

A bangare guda, talakawa ‘yan Najeriya na ci gaba da shan wahalar hauhawar farashin kayan abinci, inda tukunyar daya daga cikin shahararrun abincin kasar nan, shinkafa Jollof, yanzu za a iya kashe akalla Naira 10,00 don girkawa iyali mai mutane hudu.

Wannan ya karu da kashi 39.3% ko N2,913 akan N7,401 da ake kashewa a watan Janairun 2017 don shirya irin wannan abinci.

An samar da wannan kima ne yayin da aka kimanta nazarin matsakaicin farashin kayan masarufi da ya fito daga Ofishin Kididdiga na Kasa ta a watan Agusta 2021 wanda aka zaba cikin rahoton farashin abinci da aka fitar ranar Talata, 21 ga Satumba, 2021.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel