Ba a gama jimami kan samun matsala da Facebook ba, sai ga MTN sun shiga sahu

Ba a gama jimami kan samun matsala da Facebook ba, sai ga MTN sun shiga sahu

  • An samu matsalar sadarwa da layin MTN saboda wasu matsalolin yau da kullum na sabis
  • Kamfanin ya ba mutanen da ke amfani dashi kan wannan rashin sadarwa da aka samu
  • Har yanzu dai ba a gano musabbabin matsalar ba, amma kamfanin ya ce yana nan kam aiki akai

Miliyoyin masu amfani layin MTN a ranar Asabar sun sami tasgaron sabis a hada-hadar kiraye-kiraye, hawa Intanet da sauran bukatu.

Kalubalen, bai takaita ga jihar Legas kawai ba, saboda an sami koke-koke daga kwastomomi daga sassa daban-daban na kasar.

Ko da yake, MTN ya nemi afuwa game da matsalar, kalubalen, bisa ga bincike ya fara ne da misalin karfe 4 na yamma agogon Najeriya, The Guardian ta ruwaito.

Ba a gama jimamin samun matsala da Facebook ba, MTN sun shiga sahu
An samu matsala da layin MTN | Hoto: mtnonline.com
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

Ba a dai iya gano musabbabin kalubalen ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

Sai dai shafin yanar gizo na cibiyar sadarwar ya bayyana cewa:

“Wasu daga cikin abokan cinikinmu suna fuskantar matsalar sadarwa a yau. Muna duba wannan kuma muna matukar nadama kan duk wani rashin jin dadi da aka samu.”

Adadin masu amfani da MTN ya karu zuwa miliyan 77.3, a cewar sabon kididdigar masana'antu daga Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC).

Kamfanin sadarwar, wanda kwanan nan ya yi bikin cika shekaru 20 da kafuwarsa a Najeriya a ranar 8 ga watan Agusta, yana daukar 39% cikin 100% a kasuwar sadarwa a Najeriya.

Kalli sanarwar:

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Bayan samun matsala a Facebook, Mark Zuckerberg, ya ce bai damu da kudin da ya rasa ba ko kuma yawan masu amfani da suka yi hijira zuwa wasu kafofin sada zumunta yayin da hajojinsa suka daina aiki na tsawon sa'o'i bakwai a ranar Litinin, 4 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan Najeriya na korafin layukan MTN sun daina aiki a Abuja, da wasu jihohi

Zuckerberg, mai kamfanin Facebook wanda ya bayyana matsayinsa a shafin Facebook a ranar Talata, 6 ga Oktoba ya ce ya fi damuwa da wadanda ke dogaro da hajojinsa don cudanya da abokai da dangi.

Ya rubuta:

"Mun shafe awanni 24 da suka gabata muna bincike kan yadda za mu iya karfafa tsarinmu kan irin wannan gazawar. Wannan kuma tunatarwa ce ga yadda aikin mu yake da mahimmanci ga mutane.”

Hakanan, Zuckerberg ya ce zarge-zargen da ake yada wa na masu satar bayanai kan ayyukan Facebook ba gaskiya ba ne kuma ba su shafi Facebook da 'yan uwanta WhatsApp da Instagram ba.

A kalamansa::

"A zuciyar irin wadannan zarge-zargen shine muna fifita ra'ayin riba akan aminci da walwala. Wannan ba gaskiya bane.”

Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi

A baya mun rahoto muku cewa, wanda ya kirkiro kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Mark Zuckerberg ya tafka asarar fiye da $6,000,000,000 cikin sa’o’i kadan da dakatar da kafar, inda ya sauka kasa a jerin masu kudin duniya kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

Lamarin da ya janyo asarar ta auku ne cikin sa’o’i kadan kwatsam kafafen sada zumuntar zamani kamar Facebook, Facebook Messenger, Instagram da WhatsApp su ka tsaya cak su ka dena yin aiki.

Kamar yadda Yahoo Finance ta ruwaito, wannan lamarin da ya auku a ranar ranar Litinin 3 ga watan Oktoban 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel