Manyan laifuka 3 da suka jawo aka daure Faisal Maina shekaru 14 a gidan yari

Manyan laifuka 3 da suka jawo aka daure Faisal Maina shekaru 14 a gidan yari

  • A yau ne aka yankewa Faisal Abdulrasheed Maina hukuncin shafe shekaru 14 a gidan maza
  • Rahotanni sun bayyana yadda zaman kotu ya kaya tare da bayyana yadda batun ya faro a farko
  • A rahoton da Legit.ng Hausa ta hada, mun tattaro batutuwa uku manya da aka tuhumi Faisal akai

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, bayan shafe tsawon lokaci ana danbarwa kan bautun Faisal, da Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar sauye-sauye ta fansho a yau dai an yanke wa matashin hukunci.

Rahotanni da muke samu daga majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa, an yanke wa Faisal hukunci ne bisa aikata wasu laifuka guda uku.

An yi hukuncin ne a babban kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja a gaban mai shari'a Okon Abang, wanda ya karanto tuhume-tuhume da ake wa matashin.

Read also

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Manyan laifuka 3 da suka jawo aka daure Faisal Maina shekaru 14 a gidan yari
Faisal Maina da Mahaifinsa Abdulrasheed Maina | Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

Idan baku manta ba, Abdulrasheed Maina na gaban kotu kan batun yin sama da fadi da wasu kudaden da suka kai N2bn, lamarin da ya kai ga bincike har kan dansa Faisal.

Legit.ng Hausa ta tattaro yadda shari'ar ta kaya da kuma irin laifukan da aka kama Faisal da su.

An kama Faisal da laifuka kamar haka:

1. Halatta kudin Haram

A hujjojin da hukumar EFCC ta gabatar, an ce Faisal ya halatta kudin haram ta hanyar cin kudin da yasan haramtattu ne da mahaifinsa ya sace.

2. Hada kai wajen sace kudin al'umma

A bangare na biyu, an tuhumi Faisal da hada kai da mahaifinsa wajen kirkirar asusun banki na karya a bankin UBA domin karkatar da kudade, wanda hakan babban laifi ne a dokar kasa.

Read also

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

3. Tserewa doka yayin bincike

A sashe na uku kuwa, Faisal ya tsere zuwa kasar waje bayan ba da belinsa, wanda tuni ya daina halartar kotu don zaman shari'ar da ake gudanarwa.

Wadannan, da sauran wasu dalilai su suka jawo kotu ta garkame matashin tsawon shekaru 24 a gidan yari, amma zai kwashe shekaru 14 a ciki saboda wsau dalilai na doka, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sai dai, yayin da ake karanta hukuncin bayan alkali ya ruguza batun belinsa, Faisal ba ya nan a cikin kotu wanda mai shari'a ya ba da umarnin a kamo shi a duk inda yake.

Yadda batun belin Faisal ya kaya

A watan Fabrairun da ta gabata, EFCC ta hannun lauyanta mai gabatar da kara, Mohammed Abubakar, ya shaida wa mai shari'a Abang cewa wanda ake tuhuma ya tsere zuwa Amurka.

Mista Abubakar ya ce EFCC ta samu labarin cewa Faisal ya tafi kasar Amurka ta Jamhuriyar Nijar.

Read also

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

Wannan ci gaban ya tilasta wa alkalin kotun, Mista Abang, ya umarci wanda ya tsaya wa Faisal, Sani Dan-Galadima, wanda dan majalisar wakilai ne, da ya mika kadarar da aka yi amfani da su a matsayin beli ga doka.

Mista Dan-Galadima wanda ke wakiltar Mazabar Kaura-Namoda ta Tarayya ta Zamfara, ya ba da belin Naira miliyan 60 a madadin Faisal.

Duk kanwar ja ce

Mista Maina, mahaifin wanda ake tuhuma, wanda shi ma ake tuhuma a gaban alkalin kotun, shi ma ya tsallake belin da aka bayar a kansa bara.

Bayan umarnin da alkali ya bayar na a kamo shi, an kama Maina a Jamhuriyar Nijar, kuma an dawo da shi Abuja don ci gaba da fuskantar shari’arsa a watan Disamba na 2020.

Tuni Mista Maina ya ci gaba da zama a gidan yari tare da ci gaba da shari'ar sa a kotu.

Source: Legit.ng

Online view pixel