Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, shugaba Buhari ya gana da tsohon shugaban kasa Jonathan
  • An ce ba a san dalilin ganawar tasu kasancewar Jonathan bai magantu da manema labarai ba bayan ganawar
  • Ana kyautata zaton sun gana ne kan batun tsaron Najeriya da kuma yiyuwar zawarcin Jonathan a APC

Abuja - Jaridar Daily Trust ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa ba a san dalilin ziyarar ba saboda Jonathan bai yi magana da manema labarai ba bayan taron.

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da Goodluck Jonathan
Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da Goodluck Jonathan | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Sai dai kuma, an lura cewa tsohon shugaban, a matsayinsa na wakilin ECOWAS na musamman a Mali, yana ta yin taro akai-akai tare da Shugaba Buhari kan kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da rikici.

Kara karanta wannan

An fara taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP a Abuja

Akwai kuma rade-radin cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin kasar suna zawarcin Jonathan da tikitin takarar shugaban kasa na 2023.

Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan

A wani labarin, Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Muhammed Babandede, a ranar Juma'a ya yi bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan NIS na kokarin tsare iyakokin kasar nan.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron sirri da yayi da shuagaban kasa, Babandede ya ce NIS ta kirkiro da sabbin tsare-tsare domin duba yanayin shige da fice bakin haure a kasar nan ba bisa ka'ida ba.

Kamar yadda yace, hukumar ta samu kayan aiki masu kyau domin taimaka wa wurin fallasa jama'ar da ke zama a kasar nan ba bisa ka'ida ba bayan hatimin shigowa kasar nan nasu ya gama aiki.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Na kai karar Malami gaban Buhari, kuma bai amince da dokar ta-baci ba a Anambra - Gwamna Obiano

Asali: Legit.ng

Online view pixel