Yanzu Yanzu: An kama jagoran kungiyar IPOB a wata kasar Afrika, an saki suna da hotonsa

Yanzu Yanzu: An kama jagoran kungiyar IPOB a wata kasar Afrika, an saki suna da hotonsa

  • Bayan Nnamdi Kanu, an sake kama wani babban dan kungiyar IPOB, Chidi Uchendu, a wata kasar Afirka
  • Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, ta bayyana a shafinta na Facebook cewa an cafke Uchendu a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba
  • Ana zargin Uchendu da halartar gangamin tayar da kayar baya na Biafra da aka gudanar kwanaki

Jami'an 'yan sanda a kasar Saliyo sun cafke jagoran kungiyar yan asalin yankin Biyafara (IPOB) na Saliyo, Chidi Uchendu.

A cewar Lauretta Onochie, kamun Uchendu wanda wata majiya mai tushe ta tabbatar, ya faru ne a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba a wurin kasuwancinsa da ke Freetown.

Yanzu Yanzu: An kama jagoran kungiyar IPOB a wata kasar Afrika, an saki suna da hotonsa
An kama jagoran kungiyar IPOB a wata kasar Afrika, an saki suna da hotonsa Hoto: Lauretta Onochie
Asali: Facebook

Hadimar shugaban kasar kan harkokin yada labarai ta bayyana cewa an cafke wanda ake zargin ne saboda hannu da yake da shi wajen yada fafutukar Biyafara a kasar ta Afrika.

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

A halin yanzu yana hannun 'yan sanda har zuwa lokacin da za a gurfanar da shi.

Da ta ke mayar da martani kan wannan ci gaban, ta ce kawayen Najeriya ba za su kara yarda da 'yan ta'adda a yankunan su ba.

Hadimar Buhari ta bayyana sunayen makasan mijin tsohuwar minista

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa Lauretta Onochie, mataimakiyar shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ta bayyana cewa mambobin kungiyar IPOB ne suka kashe marigayi Chike Akunyili, mijin Dora Akunyili a ranar Talata 28 ga watan Satumba.

Onochie ta yi wannan babban zargi a shafinta na Facebook a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba.

Hadimar shugaban kasar kan harkokin yada labarai ta kara da cewa an kashe mai tsaron marigayin, wani fasto da direbansa.

Kara karanta wannan

Boko Haram sun gurgunta mulki a Neja, sun kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata

Har ila yau, Uche Mefor, barrantaccen mataimakin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, ya zargi kungiyar da kisan Dakta Chike Akunyili a jihar Anambra, ShaharaReporters ta ruwaito.

Dakta Chike shine mijin marigayi Dora Akunyili, tsohuwar Ministar Yada Labarai da Sadarwa kuma Darakta-Janar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC).

Asali: Legit.ng

Online view pixel