Osinbajo ya bayyana halin da yankunan kasar nan za su shiga idan Najeriya ta rabu

Osinbajo ya bayyana halin da yankunan kasar nan za su shiga idan Najeriya ta rabu

  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce idan Najeriya ta rabu, kowa zai dandana wahalar
  • Osinbajo ya yi kira ga 'yan jaridu da su tabbatar da sun yi aiki domin kawo hadin kai a kasar nan a maimakon raba ta
  • Dan siyasan ya tabbatar da cewa, masu hannu da shuni ba za su girgiza ba, sai dai babu shakka talaka zai matukar wahala idan aka raba kasar

Aso Villa, Abuja - Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce 'yan Najeriya ne za su wahala idan aka raba kasar nan.

Ya sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin shugabannin kungiyar 'yan jarida na kasa a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Shugabannin NUJ sun samu jagorancin shugabansu na kasa, Christ Isiguzo, TheCable ta ruwaito.

Osinbajo ya bayyana halin da yankunan kasar nan za su shiga idan Najeriya ta rabu
Osinbajo ya bayyana halin da yankunan kasar nan za su shiga idan Najeriya ta rabu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda takardar da Laolu Akande, mai magana da yawun Osinbajo ya fitar, ya ce akwai bukatar a karfafa hadin kai a kasar nan kuma ya shawarci 'yan jarida da su kasance masu kwarewa yayin sauke nauyin da ke kansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Najeriya kasar mu ce, mu 'yan jarida, 'yan siyasa ko kuma shugabannin addinai. Kasar mu ce kuma dole ne mu yi duk abinda ya dace wurin tabbatar da zaman lafiya tare da hadin kan kasar, hakan ya na da amfani," yace.

Ina godiya gare ku kan sa idon ku, kalamanku tausasa da kuke kan Najeriya da kuma yadda kuka yadda da dokoki tare da 'yancin jarida a kasar nan, TheCable ta wallafa.

"Kamar yadda na ke cigaba da fadi, wadanda muka samu damar samun ilimi, mukamai da sauransu, akwai hakkin miliyoyin 'yan Najeriya da suke cikin talauci, wadanda ba su samu dama ba, akwai hakkin su na ganin cewa ba mu bar kasar nan ta tabarbare ba.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

"Akwai kasashe masu tarin yawa da ke fuskantar kalubale kuma inda akwai wasu miyagu da ke fatan tabarbarewar kasar. Sai dai 'yan jaridunsu na aiki da gwamnati wurin tabbatar da cewa an bai wa fannin yada labarai kariya ta yadda ba a gurbata shi ba.
"Amma ina tunanin akwai matukar amfani idan aka mutunta muryoyin ku. Muryoyin ku suna da matukar amfani domin kuwa su al'umma ke sauraro kuma da su ne kasar nan za ta san makomar ta.
"Akwai matukar amfani idan aka cigaba da jaddada hadin kai a kasar nan saboda idan muka kuskura muka rabu, dukkanmu ne za mu dandana wahalar. Babu shakka masu hannu da shuni za su fita daga lamarin kuma bai zai girgiza su sosai ba. Amma kuma da yawa daga cikin mutanen mu za su wahala.
"A don haka na ke kira garemu da mu yi duk abinda ya dace wurin tabbatar da cewa ba mu rabu ba. Mu tabbatar hadin kan kasar nan shi ne a gaba kuma mu kauce wa ta'addanci da aikata laifuka."

Kara karanta wannan

Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands

Gyara Kimtsi: An nada ministan Buhari, Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi

A wani labari na daban, Sarkin Argungun, Mai Martaba Sumaila Mera a ranar Lahadi ya bai wa ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa an yi nadin sarautar a cikin fadar sarkin Argungun da ke jihar Kebbi duk daga cikin jerin shagalin ranar shakatawa da za a yi a Birnin Kebbi ranar Litinin.

A yayin jawabi wurin bikin, sarkin ya ce an bai wa ministan wannan sarautar ne saboda kwazonsa wurin karfafa kyawawan tsarin al'adun Najeriya a gida da waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel