Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga Yayin da Suka Yi Kokarin Kai Hari Zariya

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga Yayin da Suka Yi Kokarin Kai Hari Zariya

  • Gwarazan yan sanda sun cafke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne ɗauke da shanu maƙare da motar Bas a Kaduna
  • Kakakin yan sandan Kaduna, ASP Muhammed Jalige, yace jami'an yan sanda sun cafke wani sanannen ɗan bindiga da aka jima ana nema
  • Hakanan kuma, gwarazan yan sanda sun samu nasarar daƙile harin sace mutane a garin Zariya, jihar Kaduna

Kaduna - Rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa jami'anta sun cafke masu garkuwa da mutane da safiyar Lahadi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Hakazalika rundunar ta sanar da cewa gwarazan jami'anta sun sheƙe mutum ɗaya daga cikin wasu tsagerun yan bindiga da suka yi nufin sace mutane a Zariya.

Kakakin rundunar reshen jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, ranar Litinin a Kaduna.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Yan sanda sun cafke mutum 5
Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Yan Bindiga Yayin da Suka Yi Kokarin Kai Hari Zariya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jalige yace a ranar 26 ga watan Satumba, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, jami'an yan sanda sun kai ɗaukin gaggawa kan wani bayanin sirri da suka samu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta gano cewa jami'an sun samu rahoton cewa wata motar Bas maƙare da shanu da ake zargin na sata ne ta nufi wani wuri da ba'a sani ba a kan hanyar Barde–Keffi.

Yan sanda sun cafke sanannen ɗan bindiga

Jalige yace:

"Bisa wannan bayanin da muka samu, jami'an yan sanda na caji ofis ɗin Kafanchan sun kai ɗauki kuma suka samu nasarar kame motar, sun kama mutum 5."
"Daga cikin waɗanda aka cafke harda wani sanannen ɗan garkuwa da mutane, wanda hukumar yan sanda ke nema ruwa a jallo, an kwato shanu 13 a hannunsa."

Kakakin yan sandan yace waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu, yayin da aka gano shanun mallakin wani mutumi ne a ƙauyen Uddah, kuma an bashi dabbobinsa.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da taro, tsagerun Yan bindiga sun buɗe wuta kan mambobin Jam'iyyar APC

Meyafaru a Zariya kuma?

A ɗaya ɓangaren kuma, Kakakin yan sandan ya bayyana cewa jami'ai sun dakile harin tawagar yan bindiga a Zariya, ranar Litinin.

"A ranar 27 ga watan Satumba, jami'an yan sanda sun samu kiran gaggawa ta caji ofis ɗin birnin Zariya, inda aka shaida musu cewa wasu mahara sun farmaki gidan wani mutum a Nagoyi Quaters."
"Bayan samun bayanai, jami'an yan sanda tare da yan bijilanti bisa jagorancin DPO, sun kai ɗauki, inda suka fafata da maharan."
"Yayin haka, jami'ai sun samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin yan bindigan, sauran kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga a jikinsu.

Yace an kai gawar wanda aka kashe ɗakin aje gawarwaki na asibitin koyarwar jami'ar Ahmadu Bello Zariya (ABU).

A wani labarin na daban kuma Tsohon mataimakin gwamna tare da jiga-jigan APC 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Jam'iyya mai mulkin ƙasar nan ta samu koma baya a jihar Gombe, yayin da jiga-jiganta aƙalla 15 suka koma jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun hallaka yayin da miyagun yan Bindiga suka farmaki barikin Sojoji a Sokoto

Tsohon mataimakin gwamnan Gombe, Lazarus Yoriyo, yace sun ɗauki matakin ficewa daga APC ne saboda abinda ke faruwa a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel