Gwamna ya je Landan dubo Bola Tinubu, ya gano dalilin makalewarsa a kasar waje

Gwamna ya je Landan dubo Bola Tinubu, ya gano dalilin makalewarsa a kasar waje

  • Gwamnan jihar Ekiti ya ziyarci Tinubu, ya kuma bayyana abin da yasa Tinubu ke zaune a Landan
  • Ya bayyana cewa, Tinubu na fama da rashin lafiya har ma an yi masa tiyata a birnin na Landan
  • A bangare guda, ya bayyana cewa, Tinubu bai da wata alaka da zaben 2023 mai zuwa ta kowace fuska

Ekiti - Gwamna Kayode Fayemi ya musanta ikirarin cewa ya tafi Ingila kwanan nan don ziyartar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan batun zaben 2023, Punch ta ruwaito.

Gwamnan na Ekiti wanda ya zanta da manema labarai a ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba, ya ce ya ziyarci Tinubu ne saboda an yi masa tiyata kwanan nan, ya kara da cewa ba shi da alaka da tsare-tsaren zaben 2023 da ake zargi.

Kara karanta wannan

Bayan kai karar mahaifiyarsa ga EFCC, dan Ganduje ya tsere zuwa Egypt

Fayemi ya ce a matsayinsa na dattijo kuma jigo na jam’iyyar APC, Tinubu ya cancanci a nuna masa kauna da kulawa a lokutan bukata wanda shine babban dalilin da yasa ya kai masa ziyara.

Gwamna ya je Landan dubo Bola Tinubu, ya gano dalilin makalewarsa a kasar waje
Gwamna Fayemi da Bola Tinubu | Hoto:independent.ng
Asali: UGC

A cewar Fayemi game da ziyarar ta sa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An yi wa Asiwaju tiyata, kawai ladabi ne ko dabi'a irin na yankin kasar da na fito haka nan kuma gaba daya cewa lokacin da aboki ko dattijo ke fuskantar kalubalen kiwon lafiya, ba daidai bane a gare ku ku ki nuna hadin kai da goyan baya.
“Wannan shine kawai abin da ya kai mu can; mun so ne mu gana da shi a lokacin bukata kuma a matsayin dattijo, a matsayin mai ba da shawara kuma a matsayin babban jigo a cikin jam’iyyarmu ta siyasa, babu laifi a kai masa ziyarar girmamawa don duba shi don ganin halin da yake ciki kuma mun yi hakan sannan muka dawo.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

“Babu ruwansa da 2023; bari in bayyana hakan a balo-balo.”

Takarar shugaban ƙasa a 2023: Allah kadai yasan abinda ya tanazar mun a gaba, Gwamna ya magantu

Gwamnan jihar Ekiti, kuma shugaban kungiyar gwamnoni (NGF), Kayode Fayemi, yace Allah kadai yasan abinda ya tanadar masa nan gaba a siyasar 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Fayemi ya yi wannan furuci ne ranar Lahadi, yayin da yake fira da kafar watsa labarai ta Arise TV.

Tuna watan Agusta, 2020, fastocin yaƙin neamn zaɓen shugaban kasa na gwamna Fayemi suka watsu, kuma hakan ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Wanda ya dauki nauyin buga fastocin kuma ciyaman na karamar hukumar Ikere ta jihar Ekiti, Femi Ayodele, yace ya yi haka ne domin nuna goyon bayansa ga Fayemi.

Bugu da kari Ayodele ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne domin maida martani ga masu yada jita-jitar cewa yana cin dunduniyar gwamnansa.

Kara karanta wannan

Ba zai yuwu arewacin Najeriya ta cigaba da mulki har abada ba, Shina Peller ga NEF

Daga Karshe: Rarara ya rera wa masoya Buhari wakar da suka biya kudi ya rera

A wani labarin, shahararren mawakin shugaba Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya cika alkawarin da ya dauka na rera wa shugaba Buhari waka, wacce masoya shugaban suka dauki nauyi.

Shekaru kusan biyu da suka gabata Rarara ya bayyana cewa, ba zai sake yiwa shugaba Buhari waka ba har sai masoya Buhari kowa ya tura N1,000 kafin ya rera wata sabuwar wakar Buhari.

Lamarin ya jawo cece-kuce yayin da aka tura masa makudan miliyoyi, kamar yadda wasu majiyoyi suka rahoto, amma bai saki wata waka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel