Sojojin Nijar sun ceci sojin Najeriya da 'yan bindiga suka kai wa farmaki sansaninsu a Sokoto

Sojojin Nijar sun ceci sojin Najeriya da 'yan bindiga suka kai wa farmaki sansaninsu a Sokoto

  • Zakakuran sojojin kasar Nijar sun ceci sojojin Najeriya 9 da 'yan Boko Haram suka kai wa farmaki
  • Sojojin sun tsere zuwa kauyen Basira da ke yankin Hodan Roumdji a jamhuriyar Nijar a ranar Juma'a
  • A ranar Juma'an ne miyagun 'yan bindigan suka kai farmaki sansanin sojojin da ke Sabon Birni a Sokoto

Nijar - Dakarun sojin kasar Nijar sun ceci sojojin Najeriya 9 wadanda suka tsere yayin da 'yan bindigan daji suka far musu a Sokoto.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa an ceci sojin Najeriyan a Basira, wani kauye da ke kan iyaka karkashin yankin Hodan Roumdji a jamhuriyar Nijar a ranar Juma'a.

Sojojin Nijar sun ceci sojin Najeriya da 'yan bindiga suka kai wa farmaki sansaninsu a Sokoto
Sojojin Nijar sun ceci sojin Najeriya da 'yan bindiga suka kai wa farmaki sansaninsu a Sokoto. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai farmaki sansanin hadin guiwa na sojoji da ke sansanin Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka kashe jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 17 yayin harin Sokoto, Ɗan Majalisa

'Yan bindigaan sun kai farmaki Gawata da wasu kauyuka da ke yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da an kai farmakin a sa'o'in farko na ranar Juma'a, ba a samu bayanai ba har sai ranar Lahadi saboda datse layikan sadarwa a jihar Zamfara da wasu sassan Sokoto da Katsina.

Dan majalisar jihar Sokoto a matakin jiha, Aminu AlMustapha Gobir, ya tabbatar da farmakin inda yace jami'an tsaro 12 sun rasa ransu.

Hakazalika, kwamishinan tsaro na jihar, Kanal Garba Moyi mai ritaya, ya tabbatar da harin ga Daily Trust amma ya ce bai san yawan wadanda aka rasa ba.

Daily Trust ta tattaro cewa, miyagun 'yan bindigan da suka kai farmakin sun hada da na kungiyoyi biyu na jiga-jigan 'yan bindigar Zamfara irin su Halilu Sububu da Kachalla Turji.

Daga bisani, NYSC ta ce ita ta fitar da shawarar biyan kudin fansa, za ta fara bincike a kai

Kara karanta wannan

Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa

A wani labari na daban, a abinda da ya janyo wa hukuma NYSC cece-kuce, ta aminta da cewa daga cikin takardun bayanai kan tsaronta ne ga ma'aikata da kuma 'yan bautar kasa aka samu wannan shawarar wacce ta matukar tada kura.

Shawarar ta bukaci duk masu hidimar kasa da kuma ma'aikata masu kaiwa da kawowa kan manyan tituna da ke da hatsari da su sanar da iyaye, 'yan uwa da abokan arziki ko kuma wadanda za su iya biyan kudin fansarsu idan an sace su.

Hukumar ta ce ta gaano cewa tabbas wannan takardar ta gama yawo a gari amma akwai wadanda babu wannan shawarar a ciki, Premium Times ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel