Duka Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su yi muhimmin taro a kan batun harajin VAT

Duka Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su yi muhimmin taro a kan batun harajin VAT

  • A yau ake sa rai ne Gwamnonin Arewa za su yi zama game da lamarin karbar harajin VAT
  • Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Lalong yace za a yi taron ne a Kaduna
  • Gwamnonin Arewacin kasar za suyi zaman ne mako daya bayan na Kudu sun yi taro

Plateau - A yau Litinin, 27 ga watan Satumba, kungiyar gwamnonin jihohin Arewa za tayi taron gagggawa inda za a tattauna a kan abin da ya shafi VAT.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai zai sauki baki a wannan taro da za a shirya a garin Kaduna.

Gwamnan jihar Filato wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Simon Bako Lalong ne zai jagoranci ragamar zaman da za ayi a safiyar Litinin.

Kara karanta wannan

ASUU: Malaman Jami’a za su hadu da Gwamnati a kan yiwuwar sake shiga yajin-aiki

Sakataren gwamnatin jihar Filato, Farfesa Danladi Atu ya bada sanarwar wannan zama a garin Jos.

Da yake magana da Punch a ranar Lahadi, Farfesa Danladi Atu yace wasu lauyoyi sun dura kan AGF, Abubakar Malami saboda wasu maganganu da ya yi.

Ministan shari’ar kasar, Abubakar Malami SAN ya fito yana cewa gwamnatocin jihohi ba su da ikon da za su rika tattara harajin VAT a karkashin dokar kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnonin jihohin Arewa
Taron Gwamnonin Arewa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Arewa za ta dauki matsaya

Ana sa rai cewa gwamnonin Arewa za su dauki matsaya a kan wannan batu a karshen zaman na yau.

Kafin yanzu, takwarorinsu na kudu a karkashin jagorancin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu sun yi zama a kan batun, sun kuma fitar da matsaya.

A taron da suka yi a garin Enugu, gwamna Rotimi Akeredolu da sauran gwamnonin kudancin Najeriya, duk sun goyi bayan jihohi su rika tattara harajin VAT.

Kara karanta wannan

2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa

Wannan lamari ya jawo sabani a Najeriya tun da kotun tarayya ta yanke hukunci cewa jihohi ne ke da hurumin karbar harajin VAT, ba gwamnatin tarayya ba.

Rikicin Zamfara

A ranar Lahadi ne ku ka ji cewa, bincike ya nuna an samu hannun manya a kashe-kashen Zamfara da ya ci mutum 6, 000, sannan aka dauke mutane 3600.

Tsakanin 2011 da 2019, an samu marayu 25,000 da zaurawa har fiye da 6400 a Zamfara. Idan da za a dauki matakin da ya dace, gwamnati za ta tsige Sarakuna 15.

Asali: Legit.ng

Online view pixel