Bayan kai karar mahaifiyarsa ga EFCC, dan Ganduje ya tsere zuwa Egypt

Bayan kai karar mahaifiyarsa ga EFCC, dan Ganduje ya tsere zuwa Egypt

  • Rahotanni sun bayyana cewa, dan Ganduje na fari da ya kai mahaifiyarsa kara hukumar EFCC a ari na kare zuwa kasar Egypt
  • An ce ya tsere ne jim kadan bayan da ya kai mahifiyar tasa kara ga hukumar EFCC kan batun badakalar kudi
  • A halin yanzu lambarsa ta Najeriya ba ta shiga, lamarin da ke kara tabbatar da ya cilla ya bar Najeriya

Abdulazeez Ganduje, dan fari ga Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, ya tsere zuwa Egypt tare da iyalinsa bayan ya tona asirin cin hanci da ake zargin mahaifiyarsa dashi.

Mista Abdulazeez ya kai mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje kara a Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, bisa zargin cin hanci da rashawa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

Dan gwamnan ya roki cewa wani dillai ya tuntube shi don taimakawa wajen saukake siyan wasu filaye a Kano tare da wasu daruruwan dubban dalolin Amurka da akalla sun kai Naira miliyan 35 a matsayin kudin kwamisho.

Bayan kai karar mahaifiyarsa ga EFCC, dan Ganduje ya tsere zuwa Egypt
Matar gwamna Ganduje | Hoto:wikimedia.org
Asali: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa:

"Amma bayan watanni uku, (dillalin) ya gano cewa filayen da yake so kuma ya biya iyalan an raba su ga sauran masu siye sannan ya nemi a mayar masa da kudinsa."

Duk da cewa har yanzu matar Ganduje ba ta amsa gayyatar ba, amma majiyoyin tsaro sun ce za ta iya fukstar kamun jami'an EFCC tunda ba ta da kariyar kamawa da gurfanar da ita.

Majiyoyin kusa sun ce dan gwamnan ya gudu zuwa Egypt nan da nan bayan ya shigar da karar don gujewa "fushin iyayensa".

Kara karanta wannan

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

Wata majiya ta ce:

“Abdulaziz ya bar Najeriya zuwa Egypt tare da iyalansa kai tsaye bayan shigar da kara. Ya gaya mana cewa zai ci gaba da zama har sai mahaifinsa ya bar ofis.
"Ya guji iyayensa kuma ya shiga duniya tun farkon rikicin."

An gagara samun wayar Abdulazeez ta lambarsa ta Najeriya don jin ta bakinsa.

A watan Afrilu, Jaafar Jaafar, dan jaridar da ya fallasa bidiyon da aka ga gwamna Ganduje na sankama dala a aljihu ya tsere zuwa Burtaniya bayan da ya fuskanci tsangwama daga makusantan gwamnan.

Kudi kimanin N350m sun yi batan dabo daga baitul malin kotun Shari'a a Kano

Kudi Sama da N345million sun yi batan dabo daga asusun babbar kotun Shari'a a jihar Kano, a cewar rahoton gidan rediyon Freedom.

Babban Alkalin kotun Shari'ar jihar Grand Khadi Tijjani Yakasa ya tabbatar da hakan inda yace an kai karan lamarin ofishin sauraron kararraki da yaki da rashawa na Kano domin bincike.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Sakataran kotun, Haruna Khalil, ya bayyana cewa tuni an kafa kwamitin bincike domin gudanar da bincike kan lamarin.

A cewarsa, kudin da suka bata kudaden gadon mutane ne da aka ajiye a hannun kotun domin rabawa masu hakki.

Yace an gano kudaden sun yi batan dabo ne yayinda akayi kokarin cire wasu kudade, kawai sai aka ga milyan 9 kawai suka rage a asusun.

Wata sabuwa: An gano matsugunin gidan rediyon Nnamdi Kanu da ke tunzura tsageru

A wani labarin, Shekaru da yawa kenan 'yan Najeriya ke neman sanin inda 'Radio Biafra', cibiyar rediyon kafar intanet wanda ke watsa ajandar 'yan haramtacciyar kungiyar IPOB take.

Jiya, gidan talabijin na CNN, ya gano wani titi mai cike da ganye a Peckham, kudu maso gabashin London, adireshin kungiyar ta IPOB kenan, Vanguard ta ruwaito.

Gidan talabijin na CNN ya bayyana wurin a matsayin wurin da ke kusa da birni, yana mai cewa wannan wuri ne da ba a zata ba ga gidan Rediyon Biafra.

Kara karanta wannan

Kwastam za ta fara amfani da 'Drone' wajen sintiri da kama haramtattun kayayyaki

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel