Abin kunya ne Najeriya ta ke kiran kanta uwa ga Afrika, inji tsohon sarkin Kano Sanusi II

Abin kunya ne Najeriya ta ke kiran kanta uwa ga Afrika, inji tsohon sarkin Kano Sanusi II

  • Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya bayyana kokensa game da halin da Najeriya ke ciki
  • Ya ce, ya kamata Najeriya ta daina kiran kanta uwa ga Afrika saboda wasu dalilai na tattalin arziki
  • Ya bayyana cewa, Najeriya tana matsayi na 114 a fannin kirkira a duniya, wanda hakan abin kunya ne

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ll, ya ce Najeriya ta rasa kimarta a matsayin uwa a Afirka ga sauran kasashen da suka bunkasa tattalin arzikin su, Daily Nigerian ta ruwaito.

Sanusi ya ce yanzu Najeriya tana bayan sauran wasu kasashen Afirka da yawa idan aka duba ta fuskar ci gaba.

Sanusi wanda ya kasance Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya fadi haka ne a yayin rufe taron Babban Taron Zuba hannun Jari na Kaduna, mai taken, ‘KadInvest 6.0.’

Kara karanta wannan

Tattalin arzikin Najeriya ya na dab da durkushewa, Sanusi II

Abin kunya ne Najeriya ta ke kiran kanta uwa ga Afrika, Sanusi ya bayyana dalili
Tsohon Sarkin Kano Sanusi | Hoto: dailytust.com
Asali: Twitter

Ya ce yayin da Najeriya ke dogaro da danyen man fetur, wanda ke kan gabar karewa da kuma wahalar siyarwa, sauran kasashen duniya na rungumar harkar fasaha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa, cewa yayi:

“A duniya, ana sake fasalta aiki; Kashi 30 zuwa 40 cikin dari na ma’aikata a kasashen da suka ci gaba za su bukaci inganta hazakar basirarsu nan da 2030. Kuma mene ne manyan dalilan wannan sake fasalin? ICT da aiki daga nesa, wanda muka gani ko a nan yayin COVID-19.

Sanusi ya kuma bayyanacewa, nan da wani lokaci, ayyuka za su ragu kasancewar karuwar fasahar mutum-mutumi da ake yi a duniya wanda zai bar wasu 'yan Najeriya da basu san yadda ake sarrafa mutum-mutumi cikin yanayi na rashin aikin yi.

Da yake magana kan yadda tattalin arzikin ya zama tsohon yayi, Sanusi ya ce:

Kara karanta wannan

MURIC ta mayar da martani kan sauya shekar Fani-Kayode zuwa APC, ta bayyana abin da zai faru

“A gare mu a Najeriya, tattalin arzikin da muke da shi, abin da ake kira akwakwar da ke yin kwan zinare tana gab da mutuwa. Ba za ta sami kwan ba. Ci gaba ba ta ta'allaka da sinadarin carbon ba.
"Yan watanni da suka gabata, Jamus ta sami damar samar da isasshen makamashi mai sabuntawa ga duk bukatun kasar.
"A yau, muna fuskantar matsaloli wajen sayar da man Najeriya. Don haka, ba wai kawai muna samun matsalolin samarwa bane, koda mun samar, sayarwa ma aiki ne.
“Don haka, wannan yana tilasta canji, kuma a gare mu, kasar da ta dogara da mai, abubuwa na bukatar canzawa.
“Najeriya tana kan matsayi na 114 a cikin jerin kasashe masu kirkira a duniya. Mun yi kasa da sauran kasashen Afirka kamar Kanya, Rwanda da Senegal. Karshe ma, muna matsayi na 14 a yankin kuduncin Sahara na Afirka.
"Ina ganin ya kamata mu yi wannan duba na gaskiya kuma mu san inda muke a matsayin kasa. Ya kanta mu daina kiran kanmu uwa a Afirka saboda mu kato ne da kafafu duk yumbu."

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Babban Limami na Deeper Christian Life Ministry (DCLM), Fasto William Kumuyi, ya ce rashin tsaro, zalunci da azabtarwa duk za su kau yayin da Najeriya ke murnar zagayowar ranar samun 'yancin kai na wannan shekara a ranar 1 ga Oktoba.

Kumuyi ya fadi haka ne a lokacin da ya isa Abuja don yin taron gumurzu na kwanaki 5 mai taken, “Divine Solution Global”, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma yi kira da a tattauna ko a yi zaman fahimtar juna tsakanin bangarori domin samun mafita ta dindindin a danbarwar da ke likitoci mazauna Najeriya da Gwamnatin Tarayya.

Hasashe: Garabasa 4 da Shehu Sani kan iya samu ta dalilin komawa PDP

A wani labarin daban, Daily Trust ta tabbatar da ficewar Sani daga hannun hadiminsa na kusa, Malam Suleiman Ahmed a makon jiya.

Kara karanta wannan

Ku daina tsinewa shugabanninku saboda wahalar rayuwa – Sanusi ga ‘yan Najeriya

Ahmed ya ce mai gidan nasa ya sauya sheka ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, lokacin da yake ganawa da wasu jiga-jigan PDP a Kaduna.

Shin me Sanata Sani zai samu da shiga jam'iyyar adawa ta PDP?

A shekarar 2015, an zabi sanata Shehu Sani don wakiltar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Ya kasance mai sukar lamirin da kalubalantar lamurra da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel