UNGA: Buhari ya boye wa shugabannin duniya gaskiyar abinda ke faruwa a mulkinsa, Yan majalisa

UNGA: Buhari ya boye wa shugabannin duniya gaskiyar abinda ke faruwa a mulkinsa, Yan majalisa

  • Yan majalisar wakilai ƙarƙashin jam'iyyar adawa ta PDP, sun yi watsi da jawabin shugaba Buhari a wurin taron UNGA
  • Yan majalisun sun bayyana cewa kalaman da shugaba Buhari ya gabatar ga shugabannin duniya ya yi hannun riga da gaskiyar abinda ke faruwa
  • A cewar yan majalisun, komai ya tabarbare a karkashin mulkinsa, amma yace an ci karfin yan ta'adda

Abuja - Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, ya yi watsi da jawabin shugaba Buhari a taron majalisar dinkin duniya karo na 76 (UNGA), kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A jawabin da ya fitar ɗauke da sanya hannunsa, Ndudi Elumelu, a madadin yan majalisun PDP, yace sun yi nazari sosai kan jawabin da Buhari ya gabatar.

A jawabin yan majalisun sun bayyana cewa jawabin Buhari ya yi hannun riga da ainihin gaskiyar gazawar da gwamnatinsa ta yi.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi albishir a taron UNGA, yace rashin tsaro yana shirin zama tarihi a Najeriya

Shugaba Buhari a taron UNGA
UNGA: Buhari ya boye wa shugabannin duniya gaskiyar abinda ke faruwa a mulkinsa, Yan majalisa Hoto: @Buharisallau
Asali: Instagram

A gwamnatin Buhari tattalin arziki ya samu naƙasu, matsalar tsaro, da kuma wargaza walwala da jin daɗin al'umma, a cewar yan majalisun.

Wani sashin jawabin yace:

"Mun gano cewa jawabin Buhari ya saɓa wa gaskiyar abinda ke faruwa a Najeriya, bai bayyana ainihin halin da ƙasar nan take ciki ba."
"Ya ɓoye take haƙƙin yancin ɗan adam, cin hanci da rashawa, rashin jagoranci mai kyau, tsadar rayuwa, matsalar tsaro dake kara yaɗuwa da sauran matsaloli da ake fama da su ƙarƙashin mulkinsa."

Shin dagaske an ci ƙarfin yan ta'addan a Najeriya?

Yan majalisaun PDP sun ƙara da cewa rahoton da Buhari ya gabatar a UNGA ya nuna cewa an ci ƙarfin yan ta'adda a Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

"Amma a zahirin gaskiya yan ta'adda sun ƙara ƙarfi ne a ƙarƙashin mulkinsa, domin yanzun suna kaiwa sojoji hari, suna kashewa tare da sace jami'an tsaro yayin da suke mamaye ƙauyuka suna cin karen su babu babbaka."

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Shugaba Buhari ya fada a jawabin da yayi a majalisar dinkin duniya

"A matsayin mu na wakilan jama'a, bamu ji dadin jawabin Buhari ba, wanda yayi hannun riga da abubuwan dake faruwa kamar garkuwa da kashe ɗalibai a makarantun Najeriya."

Za'a saka fasahar 5G a 2022

A wani labarin kuma Fasahar 5G zai taimaka wajen rage aikata laifuka, zamu saka shi a Najeriya a 2022, Sheikh Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, yace za'a saka fasahar 5G a Najeriya a watan Janairu, 2022.

Ministan yace fasahar 5G zata taimaka matuƙa gaya wajen kare manyan kayan gwamnati, da kuma cafke masu lalata su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel