Jerin sunaye: Shugabannin Afirka masu ci guda 5 waɗanda mahaifansu suka yi shugabanci

Jerin sunaye: Shugabannin Afirka masu ci guda 5 waɗanda mahaifansu suka yi shugabanci

Al’adar mika mulki daga wannan karni zuwa wani na daga cikin ginshiƙan al’adun Afirka. Wannan al'adar da ta daɗe tana ci gaba da bayyana a zamanin nan a fadin nahiyar inda ake zaɓar gwamnatoci a bisa tsarin demokraɗiyya.

A wasu ƙasashe na Afirka kamar Gabon, Togo, da Kongo, akwai lokuta inda ubanni ke mika jagoranci ga 'ya'yansu kamar yadda yake a zamanin da.

Jerin sunaye: Shugabannin Afirka masu ci guda 5 waɗanda mahaifansu suka yi shugabanci
Jerin sunaye: Shugabannin Afirka masu ci guda 5 waɗanda mahaifansu suka yi shugabanci Hoto: Wikipedia
Asali: UGC

Ga jerin sunayen shugabannin Afirka waɗanda ubannin su ma suka kula da ragamar jagoranci a kasa:

1. Edward Akufo-Addo da Nana Akufo-Addo (Ghana)

Shugaba Nana Akufo-Addo yana kan mulki tun ranar 7 ga watan Janairun 2017. Mahaifinsa, Edward Akufo-Addo, shi ne shugaban da ba na zartarwa ba daga 1970 zuwa 1972, kasancewar shine babban alkali na uku (1966-1970).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin Afirka mafi tsufa da ke kan mulki, an bayyana matsayin Buhari

2. Ali Bongo da Omar Bongo (Garbon)

A shekarar 2009, Shugaba Ali Bongo ya karbi ragamar jagorancin Garbon daga hannun marigayi mahaifinsa, Omar Bongo, wanda ya kasance a kan mulki tun 1967. Bayan rasuwar mahaifinsa, an zabi Ali a shekarar 2009 kuma an sake zabensa a 2016.

3. Uhuru Kenyatta da Jomo Kenyatta (Kenya)

Uhuru Kenyatta, dan Jomo Kenyatta, shine shugaban Kenya na yanzu. Kasancewar shine ya kafa kasar, Jomo shine jagoranta na farko.

4. Faure Gnassingbe Eyadema da Gnassingbe Eyadema (Togo)

An yi gaggawar nada Faure Gnassingbe Eyadema a matsayin shugaban Togo a 2005 bayan rasuwar mahaifinsa, Gnassingbe Eyadema, a wannan shekarar. Gnassingbe ya jagoranci kasar daga 1967 zuwa 2005.

5. Joseph Kabila da Laurent-Desire Kabila (Congo)

Kasa da wata guda bayan kisan marigayi Shugaba Laurent-Desire Kabila a shekara ta 2001, dansa, Joseph Kabila, ya hau karagar mulki. Daga baya aka zabe shi a 2006 sannan aka sake zabensa a 2011. Bisa ga kundin tsarin mulkin 2006 na DRC, tsohon shugaban zai ci gaba da zama sanata har ya mutu.

Kara karanta wannan

NDLEA Ta Kama Dillalin Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis Na Biliyan 2.3 A Abuja

Jerin shugabannin Afirka mafi tsufa da ke kan mulki, an bayyana matsayin Buhari

A wani labarin kuma, mun kawo cewa yawancin shugabannin Afrika da ke kan mulki a yanzu suna a tsakanin shekaru 70 da doriya zuwa 80 da ‘yan kai.

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari shine na shida cikin shugabannin guda bakwai inda yake da shekaru 78 a duniya.

Shugaban na Uganda Yoweri Museveni shine na takwas a wannan jerin, inda yake da shekaru 77 a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel