Sojin Najeriya sun dakile farmakin da ISWAP suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe

Sojin Najeriya sun dakile farmakin da ISWAP suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe

  • Zakakuran dakarun sojin Najeriya da ke jihar Borno sun dakile harin da miyagun 'yan ta'addan ISWAP suka kai musu sansaninsu
  • A lokaci daya da miyagun suka kai farmakin Malam Fatori a Borno, sun kai wasu makamantan harin a sassan Yobe
  • Miyagun sun bayyana a motocin yaki amma sai da sojojin suka fatattake su har zuwa kauyen Jalingol da ke Jauro

Borno - A yammacin ranar Alhamis ne dakarun sojin Najeriya su ka yi nasarar dakile wani farmaki da 'yan ta'addan Islamic State of West Africa Province (ISWAP) suka kai sansanin soji da kuma wasu yankuna na jihohin Borno da Yobe.

PRNigeria ta gano cewa, dakarun dauke da manyan makamai sun bankado yunkurin harin da miyagun 'yan ta'addan suka kai Malam Fatori da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

Sojin Najeriya sun dakile farmakin da Boko Haram suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe
Sojin Najeriya sun dakile farmakin da Boko Haram suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

'Yan ta'addan da suka bayyana a motocin yaki da babura, zakakuran dakarun sun fi karfinsu inda suka batar da wasu daga ciki yayin da wasu suka ja da baya tare da tserewa.

Har ila yau, kusan a lokaci daya, dakarun sojin da ke jihar Yobe sun dakile wani farmakin da ISWAP ta kai yankin Babangida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiyar tsaro ta sanar da PRNigeria cewa dakarun sun fatattaki 'yan ta'addan har zuwa wurin kauyen Jalingol da ke kusa da yankin Jauro a jihar.

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

A wani labari na daban, Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yada labarai, ya ce wasu daga cikin manyan masu caccakar shugaban kasan a fili suna lallabawa Aso Rock domin cin abincin dare da shi.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, mai magana da yawun shugaban kasan ya sanar da hakan ne yayin tsokaci kan komen da Femi Fani-Kayode yayi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A makon da ya gabata bayan shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC na kasa kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gabatar da shi a gaban Buhari a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Daga 'yan jam'iyyar APC mai mulki har da na jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party sun dinga caccakarsa kan sauya shekar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel