Bidiyon Jami'an yan sanda yayinda suka damke karya kan laifin cizon dalibin jami'a a azzakari

Bidiyon Jami'an yan sanda yayinda suka damke karya kan laifin cizon dalibin jami'a a azzakari

  • Jami'an yan sanda a jihar Ondo sun damke wata karya mai suna Charlie kan laifin cizon wani dalibin jami'ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko a azzakari.
  • An ruwaito cewa wannan abu ya faru ne ga dalibin a dakin kwanan dalibai kuma aka kira yan sanda.
  • An garzaya da dalibin asibiti inda Likitoci ko kokarin ganin cewa an mayar masa da mazakutarsa

Wata karya ta shiga komar yan sanda a jihar Ondo bayan ta ciji dalibin jami'an Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko a mazakutarsa.

Instablog9ja ta ruwaito cewa karyar mai suna Charlie ta gantsari dalibin ne a harabar wajen kwanan dalibai.

Da wuri aka garzaya da dalibin asibiti kuma mutane suka gayyaci jami'an yan sanda don su kama karyar.

Bidiyon Jami'an yan sanda yayinda suka damke karya kan laifin cizon dalibin jami'a a azzakari
Bidiyon Jami'an yan sanda yayinda suka damke karya kan laifin cizon dalibin jami'a a azzakari Hoto: Instablog9ja
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

A bidiyon, an ga yadda yan bindiga sukayi awon gaba da karyar cikin motarsu.

Har yanzu dai ba'a san halin da yaron ke ciki ba.

Kalli bidiyon: Latsa gaba zuwa hoton karshe don ganin bidiyon

Mutane sun tofa albartakun bakinsu a kafafen ra'ayi da sada zumunta:

Abu Shuraem Marafa yace:

Marassa lafiyanmu nagida danawaje Allah kabasu lfy

Usman Musa Adam Alkaulahee yace:

Su matsashi yabada bayanai turoshi akayi

Aliyu Lawal Namadan yace:

Kai wllh abun dariya abun tausayi,
Nigeria kasarmu ta gado

Magaji Abdulhakim yace:

Duk cikin aiki ne sai anbiya kudin beli

Aliyu Bala Ibraheem yace:

Tab lallai akwai matsala babba azzakari kuma???

Sunusi Suraja Adamu Adam yace:

To zaro azzakarin yayi waje tagani takai Hari kokuwa ya abun yakene.

Asali: Legit.ng

Online view pixel