Yadda ni da Sanusi II muka rike darajar Naira na tsawon shekara 5 a CBN inji Farfesa Moghalu

Yadda ni da Sanusi II muka rike darajar Naira na tsawon shekara 5 a CBN inji Farfesa Moghalu

  • Farfesa Kingsley Moghalu ya bayyana abin da ya jawo Dalar Amurka ta tashi
  • Masanin tattalin arzikin ya fadi yadda CBN ta rike darajar Naira a lokacinsu
  • A halin yanzu Dala tayi tashin da ba a taba gani ba, ana saida N1 a kan N570

Nigeria - Farfesa Kingsley Moghalu ya yi bayanin yadda bankin CBN ya rike darajar Dala a lokacinsu na tsawon shekaru biyar tsakanin 2009 da 2014.

Tsohon mataimakin gwamnan na CBN ya yi wannan bayani ne a lokacin da Punch ta yi hira da shi ta kafar yanar gizo a ranar 23 ga watan Satumba, 2021.

Kingsley Moghalu ya rike kujerar mataimakin gwamnan bankin CBN a karkashin Sanusi Lamido Sanusi.

A wancan lokaci an rika canzar $1 a kan N150, amma yanzu Dalar ta tashi zuwa N570 a karkashin jagorancin gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele.

Kara karanta wannan

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

Da yake magana da ‘yan jarida, Kingsley Moghalu yace Naira tana yin kasa a kasuwar canji ne saboda rashin kafu war CBN a kasa da kuma aikin ‘yan canji.

Farfesa Moghalu
Farfesa Moghalu da Sanusi II Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene sirrin Moghalu da Sanusi a CBN?

Farfesa Kingsley Moghalu yace sun iya hana Dala tashi a kan Naira a lokacinsu saboda sun yi kokari sosai wajen jawo kamfanonin da ke zuba hannun jari.

“Mun yi kokari sosai a kan batun farashin kudin kasashen waje. Muna so mu samar da damar da za a zo daga ketare, a zuba hannun jari a tattalin Najeriya.”
“Saboda haka mun san hanyar da za ayi wannan shi ne a samar da tsayayyen farashin kudin waje.”
“Mun tabbatar cewa za ka iya shigo wa da kudinka Najeriya domin kayi kasuwanci, kuma ka maida su 100% na yadda ka zo da su, duk suna nan a na ka.”

Kara karanta wannan

ADC ta yi wa manyan Arewa kaca-kaca saboda kalamansu kan yiwuwar cigaba da rike mulki

Moghalu yace idan Daloli suna shigo wa tattalin arzikin Najeriya, farashin Dalar zai sauka zuwa kusan N400 a kasuwar canji, akasin N570 da ake canji a yau.

A baya kun ji Dalar Amurka tana ta tashi a kasuwar canji duk da babban bankin Najeriya ya dakatar da aikin Aboki Fx da nufin a rage karyewar Naira.

Manema labarai sun ziyarci kasuwar bureau de change na ‘yan canji da ke unguwar Wuse a Abuja, inda suka ga cewa ana saida kowace Dala a Naira 574.

Asali: Legit.ng

Online view pixel