FG ta gano kuma ta taka wa masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya birki, Malami

FG ta gano kuma ta taka wa masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya birki, Malami

  • Antoni janar kuma ministan shari’a, Abubakar Malami ya ce gwamnatin tarayya ta samu nasarar ganowa da kuma dakatar da masu daukar nauyin ta’addanci
  • A cewar Malami gwamnatin ta samu nasarar gano manyan mutanen da suke bai wa ‘yan ta’adda makudan kudade don su addabi al’umma
  • Dama tun watan Mayu Malami yace gwamnati ta kusa fara yanke wa wuraren mutane 400 da ake zargin masu daukar nauyin ‘yan Boko Haram ne

FCT, Abuja - Antoni Janar na kasar nan kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya ce gwamnatin tarayya ta gano kuma ta dakile duk wadanda suke daukar nauyin ta’addanci a kasar nan.

Malami a wata tattaunawa da NAN tayi da shi a birnin New York ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu nasarar gano duk wasu manyan mutanen da suke daukar makudan kudade su na bai wa ‘yan ta’addan Najeriya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Masari: Muna cin nasara kan 'yan bindiga, sojoji na gasa musu aya a hannu

FG ta gano kuma ta taka wa masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya birki, Malami
Ministan Shari'ar Nigeria, Abubakar Malami, SAN. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dama AGF tun watan Mayu ya sanar da cewa kotu za ta fara yanke wa kusan mutane 400 da ake zargin su na da alhakin daukar nauyin Boko Haram kuma cikin su akwai manyan mutanen Najeriya.

Bangarori daban-daban sun soki yadda gwamnati ta dauki tsawon lokaci ba tare da ta bayyana wadanda ake zargin ba, sai dai Malami ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tana da hujjoji kwarara akan yin hakan.

Malami ya ce gwamnatin tarayya ta shirya dakile ta’addanci

Kamar yadda Antoni janar din ya bayyana, gwamnatin atrayya a tsaye take wurin ganin ta dauki matakan kawo zaman lafiya da dakile ta’addanci a kasar nan.

Kamar yadda Malami ya ce:

“Mun samu nasarar gano wadanda suke da alhakin daukar nauyin ‘yan ta’adda.
“Mun dakatar da duk wata hanyar su ta tura wa ‘yan ta’addan kudi kuma yanzu haka mun sa ayi mana bincike mai zurfi akan su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta ce ba ta da sha'awar kunyata masu daukar nauyin ta'addanci

“Sai dai maganar gaskiya shine saboda bincike yana bukatar sirri, hakan ya sa baza mu bayyana sunayen su ba. Bama so bayyana sunayen ya shafi nasarorin da ake samu yanzu haka a binciken.”
“Yanzu dai ana jiran sakamakon bincike kuma ana samun tarin nasarori masu yawan gaske.”

Ya kara da cewa:

“Saidai wani abu da zan yi albishir da shi shine an dakilar da ba ‘yan ta’adda kudi, ko wannan kadai nasara ce mai yawa ga kasar nan."

An samu nasarori masu yawa yanzu haka a cewar Malami

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, ya ce yanzu haka an samu nasarori masu yawa dangane da ‘yan ta’addan Boko Haram:

“An rushe ‘yan Boko Haram da dama domin yanzu haka ta’addancin su a yankin arewa maso yamma ya ragu kwarai kuma kusan kowa ma shaida ne."

Sarkin Katsina ya barranta da matsayar Sheikh Gumi: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Mun cafke mutum fiye da 100 da ke ba ‘Yan bindiga bayanai a Zamfara - Matawalle

A wani labarin daba, mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ƴan bindiga sun zaɓi su rika kashe mutane 'suma bai dace a bar su da rai ba'.

Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ƴan bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa.

Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel