Duk da yi wa Yusuf Buhari fatan mutuwa, shugaba Buhari ya yafewa Fani-Kayode

Duk da yi wa Yusuf Buhari fatan mutuwa, shugaba Buhari ya yafewa Fani-Kayode

  • Femi Adesina ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya yafewa Femi Fani-Kayode bayan dawowa APC
  • Rahotanni sun bayyana yadda mambobin APC suka ji haushin dawowar Kayode zuwa jam'iyyarsu
  • Sai dai, a bangare guda, fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da suka ja shugaban kasa ya yafe masa

Abuja - Femi Adesina, hadimin shugaban kasar Najeriya kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yafewa tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma babban mai sukar gwamnatinsa, Femi Fani-Kayode (FFK).

Legit.ng ta rahoto Adesina a cikin wata kasida da ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, inda yayi kira ga membobin APC da su maida takubban su kuma su karbi FFK a jam'iyyar cikin soyayya.

Duk da yi wa Yusuf Buhari fatan mutuwa, shugaba Buhari ya yafewa Fani-Kayode
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya rubuta:

“Ba karamin tashin hankali ya haifar ba sakamakon ficewar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode (FFK), daga jam’iyyar PDP zuwa APC a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

"Wani abu mai daukar hankali, ko gishirin da aka kara wa raunin (ya danganta da gefen da kuke), shine liyafar da ya yi a Fadar Shugaban kasa ta Muhammadu Buhari, mahaifin al'umma, lamarin ya jawo cece-kuce na tsawon kwanaki."

Ya ce FFK ba wani mummunan hali yake dashi ba, kuma duk abin da ya yi, ko bai yi ba, yana jan hankali sosai.

Adesina ya lura cewa shi memba ne na APC na gaba-gaba kafin ya kaura ya koma PDP. Kuma bai tafi cikin nutsuwa ba, ya kara da cewa tsohon ministan ya yi hayaniya kafin hijirarsa zuwa PDP wanda daga baya ya zama mai tsananin kiyayya ga tsohuwar jam’iyyarsa da mambobinta.

Batutuwa kan FFK, Buhari da APC

Adesina ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF

"Tsakanin makon da ya gabata zuwa yanzu, an tono maganganu marasa dadi da FFK ya yi wa duk wanda ke da kusanci da APC. Ya fadi abubuwa kai tsaye daga bangarensa, abubuwan da dan adam zai kira abin da ba za a iya yafewa ba kuma ba za a iya mantawa ba.
"A kan Shugaba Buhari, danginsa, Yusuf Buhari wanda ya yi wa fatan ya mutu lokacin da ya yi hatsari da babur, APC a matsayin jam'iyya, gwamnati, shugabannin jam'iyyar, kungiyoyi da daidaikun mutane. Ko da wannan marubucin ma ya sha caccaka daga FFK a rubuce-rubuce da yawa.
"Haka ne, har ma ya taba cewa ya gwammace ya mutu fiye da komawa APC, amma a makon da ya gabata, ya dawo - cikin koshin lafiya. A zahiri, yawancin membobin APC masu aminci za su ji haushin cewa an sake shigar da FFK cikin jam'iyyar.
"Kuma ba wai kawai ya dawo kan mafi girman mataki bane. Ba a mazabarsa da ke Ile-Ife ta jihar Osun ba, sai dai ma nasararsa ta kasance a Fadar Shugaban kasa, tare da Shugaba Buhari da kansa a matsayin mai masaukin karbarsa."

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Yunwa ta fara fatattakar 'yan bindiga daga jihar Katsina, inji gwamna Masari

A wani labarin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya yi gargadin a kula game da komawar 'yan bindigan da yunwa ta fatattaka, zuwa garuruwa da yankuna don satar kayayyakin gona kafin lokacin girbi, Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnan ya yi gargadin ne a ranar Talata 21 ga watan Satumba, a Katsina, a wani taron shawari da ya yi da Ministan Yada Labarai da Al'adu, Lai Mohammed kan yanayin tsaro a jihar.

Taron ya samu halartar Shugabannin hukumomin tsaro na jihar, sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa da na addini, kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel