Gidaje 5 a Abuja, 2 a Legas daga cikin kadarorin tsohon Gwamna Abdulfatah da za a kwace

Gidaje 5 a Abuja, 2 a Legas daga cikin kadarorin tsohon Gwamna Abdulfatah da za a kwace

  • A ranar Laraba, hukumar AMCON ta kwace gidan tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed da ke Ilorin
  • Sai dai hukumar ta tabbatar da cewa akwai wasu gidajensa 7, 5 a Abuja da 2 a Legas da za ta kwace kwanan nan
  • Mai magana da yawun hukumar ya sanar da cewa, tsohon gwamnan da kamfanoninsa sun rike bashin N5 biliyan

A ranar Laraba, Assets Management Corporation of Nigeria (AMCON) ta kwace wasu gidaje mallakin tsohon Gwamna Abdulfatah Ahmed na jihar Kwara kan bashin da ake bin shi ha N5 biliyan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai gidaje masu tarin yawa da ke kunshe a kadarar wacce ke a adireshi No. 9A Abdulrazaq Street, GRA, Ilorin a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: AMCON ta ƙwace katafaren gidajen tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed

Gidaje 5 a Abuja, 2 a Legas daga cikin kadarorin tsohon Gwamna Abdulfatah da za a kwace
Gidaje 5 a Abuja, 2 a Legas daga cikin kadarorin tsohon Gwamna Abdulfatah da za a kwace. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda Jude Nwazor, mai magana da yawun AMCON ya sanar, ya ce hukumar ta kwace kadarar ne saboda bashin da tsohon gwamnan tare da kamfaninsa suka rike.

Ya ce dukkan kokarin da suka yi na karbo bashinsu daga tsohon gwamnan ya gagara har sai da hukumar ta kai su gaban kotu kuma aka yanke hukunci, Daily Trust ta wallafa.

Mai shari'a A.M. Liman ne ya bada umarnin daskarar da asusun bankuna tsohon gwamnan da na kamfanoninsa da suka hada Trans Properties and Investment Limited da Trans It Consulting Limited a kara mai lamba FHC/L/AMC/01/2021.

Ga wasu daga cikin kadarorin da aka lissafo kuma za a kwace:

LAGOS

No 13, Alhaji Masha Road, Surulere

No. 9 Wharf, Apapa.

ABUJA

Plot 3632, Cadastral Zone E27 of Apo

Kara karanta wannan

Hotunan shugaban EFCC yayin da ya gurfana a gaban kotu domin bada shaida

Plot 4115, Cadastral Zone F14 of Bazango

Plot 8502, Cadastral Zone E31 of Carraway Dallas

Plot 494, Cadastral Zone E31 of Carraway Dallas

Plot 719, Cadastral Zone E23 of Kyami, Abuja

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce kiyasin da ake a halin yanzu da ake yi a arewa maso yamma ya na kai da kai da yadda Afghanistan ta fada rikici, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Talata a wani taro wanda aka yi masa take da “Human Capital Development Communications Strategy Validation Meeting” wanda majalisar kula da tattalin arzikin kasa mai samun shugabancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ta shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ba gwamnan jihar Kaduna ba kadai, karamin ministan ilimi, Chukwemeka Nwajiuba, ya yi jawabi a wurin taron, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

FG ta ki halartar kotu don sauraran karar da Nnamdi Kanu ya shigar a kanta

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel