Karo na biyu, yan bindiga sun barke Otal a Abuja, Sun hallaka ɗan sanda tare da jikkata wasu

Karo na biyu, yan bindiga sun barke Otal a Abuja, Sun hallaka ɗan sanda tare da jikkata wasu

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai hari Otal a babban birnin tarayya Abuja, inda suka hallaka ɗan sanda guda ɗaya
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa Otal ɗin da karfin tsiya, kuma sun jikkata wasu mutum uku yayin harin
  • A baya, wasu miyagu sun sace tsohon mamba majalisar dokokin jihar Kogi tare da wasu mutum 8 a cikin Otal ɗin

Abuja - Yan bindiga sun kai hari Otal ɗin 'International Premium' dake Tunga Maje yankin Gwagwalada, babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa miyagun maharan sun farmaki otal ɗin ne ranar Talata da daddare.

Maharan sun yi musayar wuta da wani jami'in ɗan sanda dake wurin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Karo na biyu, yan bindiga sun barke Otal a Abuja
Karo na biyu, yan bindiga sun barke Otal a Abuja, Sun hallaka ɗan sanda tare da jikkata wasu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sahara Reporters ta tattaro cewa maharan sun jikkata mutum uku dake zaune a Otal ɗin, yayin da ɗaya daga cikinsu harsashi ya same shi.

Kara karanta wannan

Mutum 4 Sun Mutu, Yayin da Wata Motar Bas Dauke da Fasinjojin Jihar Kano Ta Zarce Kogi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin an taɓa kai hari wannan Otal ɗin?

A watan Yunin da ya gabata, wasu yan bindiga sun sace tsohon mamba a majalisar dokokin jihar Kogi, Friday Makama da wasu mutum 8 a Otal ɗin.

Wani ma'aikaci a wurin, wanda ya nemi a sakaya sunanshi yace yan bindigan sun fasa ƙofar shiga wurin da tsiya.

Ya lamarin ya faru?

Mutumin yace:

"Sun zo da misalin ƙarfe 11:00 na dare, mun tashi aiki a ranar saboda haka mun kulle ko wace kofa. Sun fasa kofa da harbin bindiga, kuma sun harbi wanda suka zo sace wa, sannan suka tafi da shi."
"Mutum uku sun jikkata, ɗaya daga cikinsu harsashi ne ya same shi yana cikin ɗakinsa. Jami'an yan sanda suna zuwa wurin tun sanda aka kawo hari na farko, kuma sun yi musayar wuta da maharan."

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Jihohin Arewa 7 sun hada kai zasu ɗauki jami'an tsaro 3,000, Masari

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, tace miyagun sun kashe jami'in ɗan sanda.

"Wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun yi kokarin kai hari amma jami'an mu suka tare su aka yi musayar wuta, a wannan lokaci ne ɗaya daga ciki ya rasa rayuwarsa."

A wani labarin na daban gwamnan Katsina, Aminu Masari, ya fusata ya bukaci sojoji su buɗe wuta kan yan bindiga koda sun shiga cikin jama'a

Gwamnan yace matakan da aka ɗauka sun jefa rayuwar yan bindigan cikin mawuyacin hali, inda a yanzun suke ƙoƙarin shigowa cikin mutane.

Amma Masari ya bukaci dakarun sojojin kada su tausaya musu koda sun shiga cikin mutane a bude musu wuta, ko da hakan zai ritsa da mutanen da ba ruwansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel