Gobara ta yi kaca-kaca da Hedkwatar hukumar NPA, dukiyoyi sun kone kurmus

Gobara ta yi kaca-kaca da Hedkwatar hukumar NPA, dukiyoyi sun kone kurmus

  • Rahotanni sun ce Hedikwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya ta NPA ta kama wuta
  • An ruwaito cewa, dukiya mai darajar miliyoyin nairori sun lalace yayin da gobarar ta kame wasu ofishoshi
  • An samu nasarar kashe gobarar, inda aka mika godiya ga hukumomin da suka kawo dauki a lamarin

Legas - Kadarori masu darajar miliyoyin nairori sun lalace sakamakon gobarar da ta tashi a Hedikwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), da ke kan titin Broad da ke birnin Legas.

An ce gobarar ta tashi ne sanadiyar dagulewar wutar lantarki a yau Laraba 22 ga watan Satumba, in ji rahoton Daily Sun.

Gobarar ta shafi ofisoshi uku a hawa na 6 na ginin amma ba a samu rahoton rasa rai ba.

Gobara ta yi kaca-kaca da Hedkwatar hukumar NPA, dukiyoyi sun kone kurmus
Hedikwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) | Hoto: maritime-executive.com
Asali: UGC

Wasu ma’aikata, wadanda suka nemi a sakaya sunan su, sun ce suna shirin fara aikin ranar ne lokacin da gobarar ta kama.

Kara karanta wannan

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

Ma'aikatan sun ce an nemi wadanda ke kan benen da abin ya shafa su kasance a wani wuri a kasa inda jami'an tsaro suka lissafa adadin wadanda ke bakin aiki.

Babban Manaja a fannin Sadarwa da Dabarun Sadarwa na NPA, Olaseni Alakija, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce jami’an hukumar kashe gobara ta NPA sun gaggauta zuwa wurin da abin ya faru, kuma nan take suka shawo kan gobarar.

Alakija ya ce bisa ka'idojin kariya, tun daga lokacin aka killace ginin da abinda ya shafa kuma ana ci gaba da bincike don gano ainihin musabbabin gobarar, Daily Trust ta ruwaito.

Abubuwan da suka lalace

Da yake bayyana irin asarar da aka tafka, Alakija ya ce an samu asarar wasu abubuwan ciki ofis, inda yake cewa:

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

“Gobarar ta shafi ofishi daya inda aka rasa na'urorin kan teburi guda 2, wasu tebura, kujeru da sauran kayan ofis. Wasu ofisoshin biyu da ke kusa da su hayaki da toka sun shafe su.

Ya kuma mika godiya ga jami'an kashe gobara da suka kawo taimakon gaggawa a kan lokaci, jami'an tsaro da suka shiga lamarin har ma dukkan masu ruwa da tsaki a wajen.

Ku tuna cewa dukiya mai darajar da ta kai biliyoyin nairori ta lalace lokacin da tsagerun 'yan daba suka cinnawa hedkwatar NPA wuta yayin zanga-zangar @EndSARS.

Majalisa ta nemi a bata rahoto kan kadarorin Janar Abacha da hankali zai dauka

A gefe guda, Majalisar wakilai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba ta nemi Kwamitin Aiwatarwa ta Shugaban Kasa (PIC) kan kadarorin da filaye mallakar gwamnati da su gabatar da rahotannin dukkan kadarorin da aka kwace daga tsoffin shugabannin Najeriya.

'Yan majalisar sun fi mayar da hankali musamman kan Janar Sani Abacha wanda Gwamnatin Najeriya ta kwato kaddarori da kudade da dama daga turai da aka ce mallakinsa ne, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bindige shugaban cocin Anglika har lahira a Imo

Dan majalisar wakilai Ademorin Kuye, shugaban kwamitin wucin gadi kan kadarorin da aka yi watsi da su ya ce majalisar tana bukatar rahoton dukkan kadarorin da aka kwato daga hannun shugabanni, musamman Janar Abacha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel