Ina alfahari da ayyukanka: Buhari ya taya Okorocha murnar cika shekaru 59

Ina alfahari da ayyukanka: Buhari ya taya Okorocha murnar cika shekaru 59

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Rochas Okorocha murnar cika shekaru 59 a duniya
  • Shugaban kasar ya yabawa Okorocha da irin namijin aikin da yake yiwa kasa da 'yan Najeriya baki daya
  • Ya kuma yabawa Gidauniyar Okorocha wacce a cewar Buhari take taimakon kowa ba nuna bambanci

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 21 ga watan Satumba ya aike da sakon taya murna ga tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, kan cikarsa shekaru 59 a duniya.

A cikin wani sako ta hannun mai taimakawa shugaban kasa a fannin yada labarai, Shehu Garba, shugaban ya jinjinawa Okorocha kan salon jagoranci mai hangen nesa da ci gaban da yake kawowa a fannoni daban-daban, inji rahoton The Nation.

Shugaba Buhari a cikin sakon da PM News ya ce ya gani ya lura cewa wannan ranar ta tunawa da haihuwar Okorocha ta zo da tarin samun nasarori, mafi mahimmancin gudummawar da ya bayar wajen gina kasa.

Kara karanta wannan

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

Ina alfahari da ayyukanka: Buhari ya taya Okorocha murnar cika shekaru 59
Shugaban kasa Muhammadu da Rochas Okorocha | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Buhari ya ce:

"Na bibiya, tare da mayar da hankali, salon jagoranci na hangen nesa, halayen siyasa da kokarin kawo ci gaba, a cikin kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati, kuma na lura da kwazon ka na gwagwarmaya ko yaushe don jin dadin marasa galihu.
“Ina yaba wa Gidauniyar Rochas, kungiyarka ta agaji, wacce ke ci gaba da karfafa gwiwa da taimakon jama'a a fadin kasar, ba tare da nuna bambancin launin fata, addini ko siyasa ba.
"A ranar cika shekaru 59 da haihuwarka, ina tare da membobin jam'iyyarmu, All Progressives Congress (APC), don yi maka fatan alheri kan tafarkin ka na hidima ga kasa da bil'adama."

Rochas: Aikin sanata ya fi karfin albashin N13m duk wata, muna bukatar kari

Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ce kusan Naira miliyan 13 da kowanne sanata ke samu a matsayin albashi da alawus-alawus bai kai wahalar aikin da 'yan majalisar ta dattawa ke yi ba.

Kara karanta wannan

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

Rochas wanda shi ma dan majalisar dattawa ne ya yi magana ne a wani taron manema labarai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba a Abuja, in ji rahoton The News.

Tsohon gwamnan na Imo wanda ke gardama kan ya kamata a rage yawan sanatoci da aka zaba daga kowace jiha zuwa uku ya ce albashin sanata ya kai kimanin naira miliyan biyu tare da alawus na gida na naira miliyan uku da sauran alawus na kusan miliyan 11.

A cewarsa:

"Amma, hakan bai isa ba saboda idan muna da sanata, ya kamata mu biya shi da kyau domin yin aikin da gaske saboda ba shi da wani aiki sai dai kuma idan muna son a yi aikin na dan lokaci ne."

Obasanjo ga Buhari: Ta'addanci ne a yi ta karbo bashi ana barin na baya da biya

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kaca-kaca da shirin gwamnatin tarayya na ciyo sabon bashi na kasashen waje, kuma ci gaba da tara bashin ta'addanci ne, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

Ya ce gwamnatin Buhari na tara basussuka ne ga masu zuwa a bayanta, yana mai bayyana hakan a matsayin "ta'addanci."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya gabatar da bukatar neman amincewa don karbo sabbin basussuka na kasashen waje na $4.054bn da €710m ga majalisar kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel