Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 26 a Zamfara

Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 26 a Zamfara

  • Sojoji na cigaba da ruwan wuta kan bindiga a dazukan arewa
  • Wannan ya biyo bayan datse layukan sadarwa a jihar Zamfara
  • Yan bindiga sun fara arcewa daga Zamfara zuwa Sokoto

Zamfara - Rundunar mayakan saman Najeriya NAF ta yi ruwan wuta kan tsagerun yan bindiga a dajin Baranda dake jihar Zamfara kuma an hallaka manyan tsageru biyar.

PRNigeria ta ruwaito cewa Sojoji sun hallaka yan bindigan ne yayinda suka kai sintiri wasu dazuka dake yankin Arewa maso yamma.

Manyan yan bindigan da aka kashe sun hada da Hussaini Rabe, Murtala Sabe, Basiru Nasiru, Sama da Isah.

An tattaro cewa wadannan yan bindiga yaran wasu kwamanda tsageru ne mai suna Abu Redde.

Wani mazauni garin wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa ruwan wutan da Sojoji suka yi a dazukan Tsaunin Sani dake Yantumaki a karamar hukumar Danmuwa yayi sanadiyar mutuwar yan bindiga akalla 26.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnati ta datse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 na jihar Sokoto

Ya kara da cewa an lalata babura 13 a harin.

Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 23 a Zamfara
Sojoji sun hallaka kasurguman yan bindiga 5, tare da mabiyansu 23 a Zamfara
Asali: Facebook

Masari: Muna cin nasara kan 'yan bindiga, sojoji na gasa musu aya a hannu

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya ce sababbin salon yaki da ta’addancin da gwamnati ta bullo da su a jihar Katsina su na aiki kuma ana samun nasarori kwarai wurin yaki da ta’addanci.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taro wanda suka yi da ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed akan matsalar tsaron a jihar.

Taron wanda ya samu halartar shugabannin tsaron jihar, shugabannin gargajiya, shugabannin siyasa da manyan malaman addinin da suke fadin jihar da sauran su.

Gwamnan ya ce dakatar da kafafen sadarwa a kananun hukumomi 13 dake jihar ya haifi da mai ido saboda an datse masu ba ‘yan bindiga bayanai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel