Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce jiharsa za ta kammala wurin kiwon shanu nan da shekaru 2
  • Gwamnan ya sanar da cewa babban bankin Najeriya ne ya taimaka da N7.5 biliyan daga cikin N10 da aikin zai lamushe
  • Malam Nasiru El-Rufai ya ce matsalar makiyaya za ta kau kuma hakan zai zama babbar hanyar kiwon dabbobi

Abuja - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Talata, ya ce jiharsa ta fara aikin naira biliyan goma na gina wurin kiwo ga makiyaya a jihar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa, El-Rufai, wanda ya zanta da manema labarai yayin wani taro da jami'an jam'iyyar APC a sakateriya jam'iyyyar da ke Abuja, ya ce nan da shekaru biyu za a kammala aikin.

Kara karanta wannan

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai
Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan ya ce babban bankin Najeriya na CBN shi ya taimaka wa jihar da kudi har N7.5 biliyan domin samun nasarar aikin, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya tuni suka dauka matsayarsu kan kiwo a sarari inda suka ce ba hanya ba ce mai bullewa a bangaren kiwon dabbobi.

"Amma kuma yin wurin kiwo ba a dare daya bane. Dole ne mu kasance masu tsari, dole ne mu kasance da shiri kuma mu tabbatar zai iya aiki. Mun dauki matsayarmu a matsayinmu na gwamnoni kuma za mu tabbatar ya yi aiki.
“A jiha ta a misali, muna kokarin samar da wurin kiwo ga makiyaya. Kuma wannan ne kadai hanyar shawo kan matsalolin. Amma kuma za a iya yin shi a dare daya?

Kara karanta wannan

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

"Wannan aikin da muke yi zai kwashi naira biliyan goma. CBN ce ke tallafa mana da naira biliyan bakwai da rabi kuma za mu kwashe shekaru biyu kafin mu kammala.
“Kuma ina fatan Fulani makiyaya su ga wannan a matsayin wata hanyar samar da dabbobi da kiwonsu a maimakon kaiwa da kawowa da su daga gonar wannan zuwa ta wani. Muna son shawo kan matsalar."

Peter Obi ga Buhari: Ka dinga daukan hoto da 'yan Najeriya masu tasiri, ba 'yan siyasa marasa daraja ba

A wani labari na daban, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daina daukar hotuna da 'yan siyasa marasa tausayi da daraja da ke sauya sheka.

Wasu fitattun 'yan siyasa sun bar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kuma sun gana da shugaban kasan a Aso Rock inda suka dauki hotuna.

Femi Fani-Kayode a makon da ya gabata ya sanar da sauya shekar da yayi zuwa jam'iyya mai mulki kuma ya dauka hotuna yayin da ya gana da shugaban kasa, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

Asali: Legit.ng

Online view pixel