Jam’iyyar PDP ta kori tsohon gwamnan Neja Aliyu a matsayin memba na BoT, ta sanar da madadin shi

Jam’iyyar PDP ta kori tsohon gwamnan Neja Aliyu a matsayin memba na BoT, ta sanar da madadin shi

  • An sauke Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja, daga mukaminsa a matsayin mamba na BoT a PDP
  • Shugaban jam'iyyar a jihar, ya nada matar marigayi tsohon gwamna Abdulkadir Kure a matsayin wacce zata maye gurbin Aliyu
  • Sakataren jam'iyyar na shiyyar arewa ta tsakiya, Maurice Tsav, ya ce an zabi Kure ne saboda irin rawar da ta taka a jihar

Minna, Niger - An kori tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu a matsayin mamba na kwamitin amintattu na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai wakiltar yankin arewa ta tsakiya.

Jaridar Punch ta rahoto cewa PDP reshen jihar ta zabi Sanata Zaynab Kure a matsayin wacce zata maye gurbin Aliyu.

Jam’iyyar PDP ta kori tsohon gwamnan Neja Aliyu a matsayin memba na BoT, ta sanar da madadin shi
Jam’iyyar PDP ta kori tsohon gwamnan Neja Aliyu a matsayin memba na BoT, ta sanar da madadin shi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa wannan na zuwa ne kusan wata guda bayan Tanko Beji ya yi nasara a matsayin shugaban jam'iyyar na jihar.

Kara karanta wannan

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

Sakataren jam’iyyar na shiyyar arewa ta tsakiya, Maurice Tsav ne ya bayyana haka a cikin sakon taya murna a ranar Talata 14 ga watan Satumba.

A cewar rahoton, jam'iyyar ta ce matar marigayi Gwamna Abdulkadir Kure ta samu takarar ne saboda soyayyarta ta uwa, jaridar Daily Post ta ruwaito.

Wasikar mai taken, Taya murna ga Uwa mai kima akan takarar PDP - BoT.

Tsav ya ce:

"Mun yi matukar farin ciki da zabin membobinku na PDP- BOT, da amanar da jam'iyyar ta dora muku.
"Na rubuta a madadin shugaba, Hon. Theophilus Dakas Sham, shugabanci da mambobin PDP na shiyyar arewa ta tsakiya don taya ki murnar zabar ki da kuma amincewa da ke a matsayin memba na PDP-BoT mai wakiltar shiyyar arewa ta tsakiya.”

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Ta wannan nadin, Kure ta maye gurbin Aliyu wanda ya shafe shekaru da dama yana rike da mukamin.

Wasiƙar ta ci gaba da cewa:

“Tabbas, wannan sabon aikin zai samar maki da wani dandamali don ƙara shimfidar ki na soyayyar uwa da muka san ki da shi a cikin jam’iyya.
“Soyayyarki da halayenki sun sanar da dalilin nadin baki ɗaya tare da amincewa da ke cikin memba na PDP-BOT a taron ƙungiyar na shiyya wanda aka yi ranar 8 ga Satumba, 2021 a Abuja. Muna da yakinin cewa za ki sanya mu alfahari a cikin BOT.”

APC za ta wargaje idan aka fito da ‘Dan takarar Shugaban kasa daga Arewa inji Okorocha

A wani labarin, mun kawo cewa a ranar Litinin, 20 ga watan Satumba, 2021, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya fara nuna tsoronsa game da kai takara Arewacin Najeriya.

Jaridar Punch ta rahoto Rochas Okorocha yana cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta bangare kaca-kaca, muddin aka hana ‘yan kudu tikitin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

2023: APC da PDP na cikin sabon matsala, Ghali Na'Abba da Utomi na shirin bayyana sabuwar kungiyar siyasa

Sanata Rochas Okorocha ya kuma ba gwamnati shawarar yadda za ta shawo kan matsalar ta da shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel