Allah ya yiwa Matar Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, gwamnan Bauchi yayi ta'aziyya

Allah ya yiwa Matar Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, gwamnan Bauchi yayi ta'aziyya

  • Babban Malamin addini, Sheikh Dahiru Bauchi yayi rashin Matarsa
  • Gwamnan Bauchi ya kai masa gaisuwar ta'aziyya
  • Gwamnan yayi addu'an Allah ya jikanta da rahama

Allah ya yiwa Hajiya Zainab, matar babban Malami, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, rasuwa.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad AbdulKadir, ya bayyana hakan yayinda ya kai gaisuwar ta'aziyya wa babban Malamin a gidansa.

Gwamna Bala ya kai ziyaran ne ranar Lahadi, 19 ga Satumba 2021.

A cewarsa:

"Ina jimamin mutuwar Hajiya Zainab, matar Sheikh Dahiru Usman Bauchi."
"Jiya na kai gaisuwar ta'aziyya bisa wannan babban rashi. Ba zamu taba manta ire-iren abubuwan da Hajiya Zainab tayi ba."

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a kudancin Kaduna

"A madadin al'umma da gwamnatin jihar Bauchi, ina yiwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi da iyalinsa ta'aziyya bisa wannan rashi."

Matar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ta rasu, gwamnan Bauchi yayi ta'aziyya
Allah ya yiwa Matar Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa, gwamnan Bauchi yayi ta'aziyya Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Mataimakin Shehu Dahiru Bauchi, Sheikh Umar Sulaiman Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Wannan ya biyo bayan mutuwar Sheikh Umar Sulaiman, mataimakin Sheikh Dahiru Bauchi.

Sheikh Sulaiman ya rasu ne ranar Litinin yana da shekara 76 a duniya bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya.

Ɗan marigayin, Khadi Mustapha Suleman, wanda ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa ga wakilin dailytrust, yace a halin yanzu ana shirye shiryen yi masa jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel