APC ta gindaya wa FFK sharuddan da zai cika kafin ta gama amincewa da shi

APC ta gindaya wa FFK sharuddan da zai cika kafin ta gama amincewa da shi

  • Jam’iyya mai mulki, APC ya lissafa wa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode sharuddan da zai cika kafin ta gama amincewa da shi
  • Kamar yadda darekta janar na kungiyar gwamnonin APC, Dr Salihu Moh Lukman ya ce, wajibi ne FFK ya yi rijista da shugabannin jam’iyyar na gundumar sa da jihar sa
  • Ya kara da cewa wajibi ne ya bayyana amincewar sa da girmamawa ga ra’ayoyin shugabanni da ‘yan jam’iyyar kafin ta amince da shi dari bisa dari

FCT, Abuja - Jam’iyya mai mulki a Najeriya, APC ta lissafo wa Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode tarin sharuddan da tace wajibi ne ya bi don ta amince da shi dari bisa dari.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, darekta janar na kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, Dr Salihu Moh Lukman ya ce, wajibi ne FFK ya tafi wurin shugaban jam’iyyarsa na gunduma da kuma shugabannin APC na jiharsa ya yi rijista kuma ya amince tare da girmama ra’ayoyin duk wasu shugabanni da ‘yan jam’iyyar kafin ya zama cikakken dan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF

APC ta gindaya wa FFK sharuddan da zai cika kafin ta gama amincewa da shi
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode. Hoto: Femi Fani Kayode
Asali: Facebook

DG din PGF din ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Lahadi, 19 ga watan Satumba, inda ya ce mambobin jam’iyyar da dama sun hassala akan yadda shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya shirya wa FFK babbar liyafa a lokacin da ya bar PDP ya koma APC.

Kamar yadda takardar, mai taken: ‘Shirin yi wa manyan mutanen da suka shiga APC da sauran su na 2023’ ta zo:

“Babban kalubalen da jam’iyya take fuskanta wurin yi wa manyan mutane rijista cikin ta kamar Fani-Kayode, ita ce tabbatar da cancantar da wadanda ta yi wa rijista. Ya za ayi jam’iyya ta tabbatar da sababbin manyan mutanen da suka shigo ta za su iya kwantar da kan su don jam’iyya ta tankwasa su ko kuma sun shiga ne don su tankwasa jam’iyyar?

Kara karanta wannan

Jonathan zai yi caca idan ya bar PDP saboda ya samu tikitin 2023 inji Kungiyar Gwamnonin APC

“Wajibi ne Fani-Kayode ya kama kan shi a jam’iyya da kuma kasa baki daya. Kada ya kuskura ya yi tunanin ya shigo APC ne don ya yi yadda ya ga dama ko kuma ya canja wani abu na jam’iyya.
“Wajibi ne ya tsare mutuncin kan sa kuma ya bi duk wasu dokokin jam’iyya. Don haka wajibi ne a ba shi kundin tsarin jam’iyyar APC ya karanta nan kusa.”
“Akwai matsalolin da zasu iya taso wa na bukatar ya yi aiki da mambobin jam’iyya musamman akan matsalolin kasa, wajibi ne ya girmama kowa kuma ya jure. Sannan shigowar sa jam’iyya yana nufin zai yi aiki tukuru wurin hadin kan kasa komai banbancin sa da wani.
“Wajibi ne Fani-Kayode ya girmama shugabanni da ‘yan jam’iyyar APC. Hakan ba ya nufin ya amince da komai, a’a kawai dai ya nuna girmamawa ga kowa. Kada ya kuskura ya fara neman hanyar rabuwar kawunan jama’a."

Kara karanta wannan

Jigon APC a Kano ya yi tir da tarbar da Buhari, APC suka yi wa Fani-Kayode a fadar Aso Villa

Wajibi ne ya yi rijista da gundumar sa da jihar sa

“Idan har ya kuskura hakan ta faru, jam’iyya za ta hukunta shi bisa yadda kundin tsarin ta ya tanadar. Don haka wajibi ne ya yi rijista da shugaban jam’iyya na gundumar sa har da jihar sa kuma ya hada kai dasu,” kamar yadda LIB ta ruwaito takardar ta bayyana.
“Babban abinda ya dace shi ne manyan mu su gwada gaskiyar shigar Fani-Kayode jam’iyya. Su gwada shi ta hanyoyin daban daban. Su tabbatar da gaskiyar sa na yin aiki wurin taimakon jam’iyya tun daga jihar Osun."

Tsohon Minista Mai Sukar Gwamnatin Buhari, Fani-Kayode ya koma Jam'iyyar APC

Tun a baya, mun kawo muku cewa, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa.

Shugaban kwamitin riko na APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da Fani-Kayode ga shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis kamar yadda kakakin Buhari Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel