'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

  • Rahotanni sun bayyana cewa, alalla 'yan sanda uku wasu 'yan bindiga suka kashe a jihar Anambra
  • Hakazalika, wasu 'yan sanda sun jikkata sakamakon harin, duk da cewa rundunar 'yan sanda ba ta tabbatar ba
  • Haka kuma an kone motar sintirin 'yan sandan kurmus bayan hallaka mutanen da ke cikinta

Anambra - Akalla ‘yan sanda uku aka kashe a garin Onitsha, jihar Anambra sakamakon harin 'yan bindiga.

Lamarin ya faru ne a hanyar Ukaegbu/Ezeiweka a Onitsha a safiyar Lahadi 19 ga watan Satumba, 2021.

An kuma kona wata motar sintiri kurmus ta jami'an da suka mutu.

Wakilin Daily trust ya tattaro cewa wasu ‘yan sanda biyu sun jikkata a harin.

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta
'Yan bindiga dauke da makamai | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

Wani ganau ya tabbatar da faruwar lamarin amma jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda na jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce har yanzu ba a sanar da shi ba batun ba.

Ana ci gaba da kai hare-hare kan jami'an tsaro a Kudu maso Gabas, lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dama na 'yan sanda.

Rundunar ‘yan sandan ta zargi haramtacciyar kungiyar ta'addanci ta IPOB da kai wasu hare-hare a yankunan.

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

Wasu 'yan bindiga sun sace dalibai 10 na Jami'ar Jihar Abia, Uturu (ABSU) a hanyar Ihube zuwa ABSU, Daily Sun ta ruwaito.

Sace daliban na zuwa ne makonni bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da malaman jami’ar uku a kan hanyar Uturu/Isuikwuato.

Lamarin wanda rahotanni suka ce ya faru tsakanin karfe 5 na yamma zuwa 6 na yamma a ranar Asabar, ya jefa al’ummar jami’ar cikin rudani.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun sako karin dalibai 10 cikin yan makarantar Bethel Baptist a Kaduna

An ba da rahoton cewa motar bas ta jihar Abia da ke jigilar fasinjoji zuwa makarantar, SUV da mota kirar Hilux mallakar wani kamfani an same su babu kowa a ciki a wurin da lamarin ya faru, abin da ke nuni da cewa ba daliban kadai aka sace ba.

Wata majiyar tsaro ta ce kawo yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba.

Mazauna a Sokoto sun hallaka 'yan ta'adda 6, sun kone gawarwakinsu kurmus

Akalla 'yan ta'adda shida, wadanda aka fi sani da 'yan fashin daji, mazauna kauye suka kashe a garin Tangaza na jihar Sokoto, Daily Nigerian ta ruwaito.

An rahoto cewa 'yan ta'addan sun sace mutane biyu a garin tare da yin watsi da tayin kudin fansa a makon da ya gabata.

Bayanai sun ce, duk da haka, 'yan ta'addan sun dage kan cewa sai sun kashe wadanda suka sacen don daukar fansa kan hare-haren da sojoji ke ci gaba da kaiwa a maboyarsu, kuma sun yi hakan.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun halaka rai 1, sun yi garkuwa da wasu a Sokoto

Asali: Legit.ng

Online view pixel