'Yan Boko Haram sun sace tarakta 5 sun banka wa 2 wuta a Yobe

'Yan Boko Haram sun sace tarakta 5 sun banka wa 2 wuta a Yobe

  • Wasu miyagu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun sace tarakta biyar tare da kurmushe biyu
  • An gano cewa 'yan ta'addan sun shiga kauyen Ngelbuwa da ke karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe
  • Sun bi sako da lunguna inda suka san akwai tarakta tare da kai wa direbobin farmaki kuma suka kwace

Gujba, Yobe - Wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun yi awon gaba da tarakta biyar tare da kone wasu biyu a Ngelbuwa da ke karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wani mazaunin garin mai suna Kyari Konto, ya ce 'yan ta'addan sun kutsa garin inda suka dauka wani mazaunin garin wanda suka umarcesa da ya nuna musu gidajen da manoma ke da tarakta.

Shugaban wata kungiyar arewa maso gabas, reshen jihar Yobe, Nuhu Baba Hassan, ya bayyana cewa an sace taraktoci uku da suke mallakin kungiyar reshen jihar Borno da Yobe.

Kara karanta wannan

Yan ta’addan da ke tserewa daga Zamfara sun kafa tuta a kauyukan Kaduna 2

'Yan Boko Haram sun sace tarakta 5 sun banka wa 2 wuta a Yobe
'Yan Boko Haram sun sace tarakta 5 sun banka wa 2 wuta a Yobe. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce taraktan da ke karkashin ikonsa duk an kwace daga hannun matukin yayin da aka nuna masa bindiga.

Shugaban ofishin 'yan sandan yankin Buni Yadi, Bitrus Mamuda Saleh, ya tabbatar da aukuwar lamarin, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Ya ce Muhammad Mustafa, shugaban NECAS reshen jihar Borno, ya ruwaito yadda 'yan ta'addan Boko Haram suka kai wa direbobin tarakta na kauyen Ngelbuwa da ke Gujba hari kuma suka sace tarakta hudu mallakin gwamnatin jihar Borno.

Ya ce 'yan ta'addan sun kara da banka wa taraktocin NECAS biyu wuta.

Zan kama ku da alhakin duk wani farmaki da aka kai barikin ku, COAS ga Kwamandoji

A wani labari na daban, Laftanal Janar Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa, ya ce duk wani farmaki da aka kai bariki, babu shakka kwamandan barikin zai kama da laifi. Ya sanar da hakan ne yayin rufe taron shugaban sojin kasa da aka yi, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Janar Faruk Yahaya: Za mu ji da 'yan bindiga da yaren da suke fahimta

Shugaban sojin kasan ya yi kira ga kwamandoji da su tabbatar da cewa sun kasance a shirye kuma suna sa ido a kowanne lokaci domin guje wa farmakin ba-zata.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya kara da cewa, halin baya-baya a bangaren wasu kwamandoji abu ne da ba zai lamunta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel