Da dumi: Kotu ta umurci Likitoci su janye daga yajin aiki

Da dumi: Kotu ta umurci Likitoci su janye daga yajin aiki

  • Bayan kimanin watanni biyu, kotu ta umurci Likitoci su koma bakin aiki
  • Gwamnatin tarayya ta gaza sulhu da Likitoci tun bayan tafiyarsu yajin aiki
  • Alkalin kotun yace yan Najeriya zasu cigaba da mutuwa idan Likitoci basu koma aiki ba

Abuja - Kotun ma'aikatan Najeriya ta umurci Likitocin kungiyar Likitoci masu neman kwarewa (NARD) su dakatar da yajin aikin da sukeyi ba tare da bata wani lokaci ba.

Likitocin sun fara yajin aiki ne ranar 1 ga Agusta bisa rashin biyansu albashi da kuma sauran wasu dalilai.

Majalisar wakilai tayi yunkurin sulhu tsakanin bangarorin biyu amma abin ya ci tura.

Sakamakon haka gwamnatin tarayya ta shigar da kara kotu inda ta bukaci a tilastawa Likitocin dakatad da yajin aikin.

Lauyan Likitocin, Robinson Ariyo, ya bayyanawa kotu cewa abinda gwamnatin tarayya ke bukata wajen kotu take hakkin likitocin ne.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Kutsa Supermarket Suka Harbe Wani Lauya Har Lahira

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da dumi: Kotu ta umurci Likitoci su janye daga yajin aiki
Da dumi: Kotu ta umurci Likitoci su janye daga yajin aiki Hoto: Resident Doctors

A cewar rahoton TheCable, Alkalin kotun, Bashir Alkali, yace:

"Lauyoyin gwamnati sun yi bayanin cewa idan ba'a amsa bukatarsu ba, yan Najeriya da dama zasu rasa rayukansu, musamman yanzu da ake fama da dawowar cutar COVID-19 karo na uku kuma mutane na mutuwa sakamakon rashin kasancewar Likitoci a kotu."
"Na yi imanin cewa idan kotu bata sa baki yanzu ba, babu adadin kudin da zai iya dawo da rayukan yan Najeriya da za'a rasa idan Likitoci suka cigaba da yakin aiki."
"Saboda haka na amince da bukatar gwamnati kuma na basu gaskiya."
"Hakazalika, ina umurtan dukkan mambobin kungiyar Likitoci a jihohin Najeriya su dakatar da yajin aikin da suka fara ranar 2 ga Agusta 2021 da wur-wuri kuma su koma aiki kafin yanke hukunci na karshe kan lamarin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel