Yan ta’addan da ke tserewa daga Zamfara sun kafa tuta a kauyukan Kaduna 2

Yan ta’addan da ke tserewa daga Zamfara sun kafa tuta a kauyukan Kaduna 2

  • Rahotanni sun kawo cewa ’yan ta’addan da suka guje wa luguden wuta da sojoji ke yi a Jihar Zamfara, sun fara yin sansani a wasu kauyukan Jihar Kaduna guda biyu
  • A yanzu haka, an ce maharan sun kafa tuta a kauyukan Saulawa da kuma Damari, dukkansu a Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar
  • Sai dai Kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige ya ce ba su sami rahoton kafa tutar a kauyukan ba, amma ya ce suna aiki da sauran hukumomin tsaro wajen magance kalubalen

Kaduna - 'Yan ta'adda da ke tserewa ayyukan soji a jihar Zamfara sun mamaye garuruwan Saulawa da Damari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Majiyoyi da yawa sun tabbatar wa Daily Trust cewa daruruwan 'yan bindigar kan babura da ake zargi mambobin kungiyar ta'adda ta Ansaru ne sun isa garuruwan biyu sannan daga baya suka kafa tutoci a kauyukan Damari da Saulawa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina

Yan ta’addan da ke tserewa daga Zamfara sun kafa tuta a kauyukan Kaduna 2
Yan ta’addan da ke tserewa daga Zamfara sun kafa tuta a kauyukan Kaduna 2 Hoto: The Nation
Asali: UGC

Damari da Saulawa suna daga cikin ƙauyuka da yawa da ke cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari da 'yan ta'adda da 'yan fashi suka mamaye ba tare da kasancewar jami’an tsaro ba.

Majiyoyi sun ce a 'yan shekarun da suka gabata ne garuruwan biyu suka kulla yarjejeniya da 'yan fashi don ba su damar yin noma yayin da aka ba 'yan fashi damar shiga kasuwanni da sauran abubuwan more rayuwa a cikin garuruwan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, yarjejeniyar ta lalace a cikin watan Fabrairu lokacin da 'yan bindiga suka mamaye garuruwa da dama ciki har da Saulawa da Damari suka kuma kashe mutane da dama.

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, wani shugaban matasa daga garin Dogon Dawa na Birnin Gwari ya ce wasu mazauna Damari sun yi ta tserewa suna komawa Zariya don tsira yayin da wasu suka sauya wa iyalansu matsuguni inda maza suka rage a garin don yin noma.

Kara karanta wannan

Janar Faruk Yahaya: Za mu ji da 'yan bindiga da yaren da suke fahimta

Ya ce:

"Sama da 400 daga cikinsu sun iso a ranar Talata, sun karbe Saulawa da Damari sannan kuma suka kafa tutocinsu, ba su kai hari kan kowa ba amma mutane suna tsoro kuma suna barin garuruwan."

Hakanan, wani mai siyar da mai a Dogon Dawa ya tabbatar da kasancewar baƙuwar ƙungiya a ƙauyen Saulawa sannan ya tabbatar da cewa mutanen ƙauyen suna ficewa daga ƙauyukan zuwa Karau-Karau, Dogon Dawa da Zaria.

“Yayin da muke magana, membobin kungiyar da muke zargin membobin Ansaru ne har yanzu suna cikin kauyen Saulawa da Damari kuma rahotanni daga wadancan kauyukan shine cewa an kafa tutoci biyu; daya a Damari, daya a Saulawa. ”

Ya ce baya ga yankin Damari, tsohon Kuyello a karamar hukumar guda ya zama yanki mai hatsari kamar yadda kungiyar ta yi amfani da mummunan yanayin don aiwatar da munanan ayyukansu, suna wa'azi ga mazauna yankin a kokarin su na son dawo da su cikinsu.

Kara karanta wannan

An bankado sabbin mafakar ‘yan bindigar Zamfara da ke tserewa

Sai dai kuma kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige ya ce rundunarsu ba ta sami rahoton kafa tutar a Damari da Saulawa ba, amma ya ce suna aiki da sauran hukumomin tsaro wajen magance kalubalen.

'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi

A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta nemi hukumomin tsaro a Kaduna da su kasance cikin shirin ko ta kwana kan yiwuwar kai hare-hare, Sahara Reporters ta ruwaito.

Ta bayyana cewa shugabanni da dakarun kungiyar ‘yan ta'adda na Boko Haram sun koma wani daji a Kudancin Kaduna daga Dajin Sambisa.

A cikin wata sanarwa da jaridar Peoples Gazette ta gani, an ce yan ta’addan sun kaura daga dajin Sambisa a jihar Borno zuwa dajin Rijana da ke karamar hukumar Chikun ta Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel