Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso Rock

Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso Rock

  • A jiya Alhamis ne shugaban hukumar EFCC ya yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasa ta Aso Villa
  • Ya sanar da yadda aka hanzarta kai shi asibiti amma likitoci suka sanar da shi cewa rashin ruwa ne matsalarsa
  • Daga nan kai tsaye ya ce ya koma ofishinsa inda daga bisani ya yada zango a gidansa, ya na cikin koshin lafiya

FCT, Abuja - Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya bayyana abinda ya faru yayin da aka gaggauta fitar da shi daga fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Daily Trust ta ruiwato yadda ya yanke jiki ya fadi a wani taron da National Identity Management Commission (NIMC) ta shirya a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Bawa: Cikakken bidiyon lokacin da shugaban EFCC ya yanke jiki ya fadi a Aso Villa

Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso Rock
Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso . Hoto daga EFCC
Asali: Facebook

Bawa ya na tsaka da yin jawabi ne lokacin da ya kasa cigaba kuma ya koma kujerarsa.

Daga bisani, wasu daga cikin jama'ar da ke wurin da suka hada da ministan sadarwa, Ali Isa Pantami ne suka raka shi har mazauninsa.

Amma duk da haka sai da ya yanke jiki ya fadi kuma aka gaggauta fitar da shi daga fadar shugaban kasan, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin jawabi a shirin siyasarmu a yau na gidan talabijin din Channels bayan sa'o'i kadan, Bawa ya ce an kai shi asibiti kuma likitoci sun ce rashin ruwa ne ya janyo mishi hakan.

"A yayin jawabin da na ke bada wa yayin da ake taron da National Identity Management Commission (NIMC) ta shirya, na samu jiri sosai kuma hakan yasa na bar kan mumbarin."

Kara karanta wannan

Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

"Kai tsaye asibiti muka wuce inda likitoci suka tabbatar min da cewa komai lafiya amma rashin ruwa ne ya kawo hakan, Don haka ya zama dole in dinga shan ruwa mai yawa.
"Daga nan asibitin ban bata lokaci ba, na koma ofishi na kuma yanzu haka ga ni na dawo gida."

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

A wani labari na daban, rundunar sojin sama ta Najeriya ta bayyana cewa ita ke da alhakin sakin wa jama'ar kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe bama-bamai ta jirgin yaki bisa kuskure.

Daily Trust ta ruwaito yadda a kalla mazauna kauyen takwas suka rasa rayukansu, wanda Air Commodore Edward Gabkwet, mai magana da yawun rundunar ya musanta da farko.

A yayin martani kan lamarin, Gabkwet ya ce:

"Wannan wallafar ta Twitter babu gaskiya a cikin ta gaba daya. A karon karshe da NAF ta kai samame ta jirgin yaki a jihar Yobe ba karamar hukuma Yunusari ba ne. Kuma ranar 5 ga watan Satumba ne. Babu bam ko wani makami da aka wurga. Nagode."

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya - EFCC

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel