Mayaudarin dan Oduduwa: Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki Fani Kayode bayan komawa APC

Mayaudarin dan Oduduwa: Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki Fani Kayode bayan komawa APC

  • Malam Ahmad Gumi ya fadi ra'ayinsa kan sauya shekar Fani-Kayode APC
  • Gumi yace ai tuni ya san Fani-Kayose mayaudari shi yasa ko tankasa ba ya yi
  • Femi Fani-Kayode ya sauta sheka jam'iyyar APC ranar Alhamis

Shahrarren Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa tuni ya san Femi Fani Kayode mayaudari kuma makaryacin banza ne.

Gumi yayi martani ne kan sauya shekar Femi Fani Kayode jam'iyyar All Progressives Congress APC daga Peoples Democratic Party PDP a shafinsa na Facebook

A cewar Gumi, Fani-Kayode dan damfara ne kuma wuta zai shiga idan bai tuba ba.

Gumi yace:

"Tun da dadewa nike banza da mayaudarin Oduduwa lokacin da yake suka na saboda na sani sarai mayaudari ne kuma makaryaci ne."

Kara karanta wannan

Yau ce rana mafi muni a tarihin siyasata, in ji hadimin Buhari yayin da Fani-Kayode ya koma APC

"Lokaci yazo yanzu kuma Alhamdulillahi, yanzu duka zage-zagensa sun zama tarihi."
"Allah kadai ya san wani wuta cikin Jahannama bakwai wannan madamfarin zai shiga idan bai tuba ba."

Mayaudarin dan Oduduwa: Ahmad Gumi ya caccaki Fani Kayode bayan komawa APC
Mayaudarin dan Oduduwa: Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki Fani Kayode bayan komawa APC Hoto: Aso Rock Villa
Asali: UGC

Tsohon Minista Mai Sukar Gwamnatin Buhari, Fani-Kayode ya koma Jam'iyyar APC

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasa.

Shugaban kwamitin riko na APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da Fani-Kayode ga shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis kamar yadda kakakin Buhari Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

Femi Fani-Kayode, ya sha alwashin tarkata gwamnonin jihohin Oyo, Bauchi da na Enugu zuwa jam'iyya mai mulki bayan komawarsa a yau.

Kara karanta wannan

Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

Fani-Kayode wanda ya zanta da manema labarai, ya ce lokaci yayi da ya dace ya hada kai da shugaban kasa wurin ciyar da Najeriya gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel