Bawa: Cikakken bidiyon lokacin da shugaban EFCC ya yanke jiki ya fadi a Aso Villa

Bawa: Cikakken bidiyon lokacin da shugaban EFCC ya yanke jiki ya fadi a Aso Villa

  • Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya fuskanci kalubalen rashin lafiya a fadar shugaban kasa
  • Rahotannin da ke bayyana sun bayyana cewa, Bawa ya samu kula yadda ya dace daga kwararrun masana lafiya a Abuja
  • Shugaban hukumar yaki da rashawan ya na daya daga cikin masu jawabi a shagalin National Identity Day da a ka yi a Villa

FCT, Abuja - Wani bidiyo ya bayyana wanda ke nuna lokacin da shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis.

Njenje Media TV ta wallafa bidiyon a YouTube da kuma shafin Instagram na jaridar. Ya nuna yadda shugaban EFCC ya fara ganin jiri yayin da ya ke magana a taron.

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Abdulrasheed Bawa yana cikin koshin lafiya - EFCC

Bawa: Cikakken bidiyon lokacin da shugaban EFCC ya yanke jiki ya fadi a Aso Villa
Bawa: Cikakken bidiyon lokacin da shugaban EFCC ya yanke jiki ya fadi a Aso Villa. Hoto daga Njenje Media TV
Asali: UGC

Kamar yadda bidiyon ya nuna, a yayin da ya ke jawabi ne kwatsam ya fara magana kuma ya tsaya na 'yan dakiku ba ya cewa komai.

Daga bisani ya fara ganin jiri sannan ya rufe idanunsa tare da rufe fuskarsa da tafin hannunsa.

Ya sanar da masu sauraronsa cewa ba zai iya cigaba da jawabi ba, daga nan ya bar kan mumbarin, ya zauna kan kujerarsa inda daga bisani ya fadi kasa.

A take cike da gaggawa aka fitar da shugaban EFCC daga dakin taron inda ya samu rakiyar ministan sadarwa, Isa Ali Pantami.

Ga bidiyon mai tsawon mintuna hudu da dakika goma sha biyar.

Da duminsa: Majalisar jihar Kano ta amince da bukatar Ganduje ta karbo bashin N4bn

A wani labari na daban, majalisar jihar Kano ta amince wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya karbo bashin N4 biliyan da ya ke nema domin kammala ayyukan wutar lantarki na Tiga da Challawa.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya yanki jiki ya fadi yayin da yake magana a dakin taro

Daily Trust ta ruwaito cewa, an amince da karbo bashin ne yayin zaman majalisar wanda ya samu shugabancin kakakin majalisar jihar Kano, Ibrahim Chidari.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da aka mika wa daraktan yada labarai na majalisar, Uba Abdullahi, wanda ya ce majalisar ta zauna kan al'amarin bayan kakakin ya karantowa majalisar da gwamnan ya tura musu.

Kamar yadda yace, shugaban masu rinjaye na majalisar yayi kira ga majalisar da su duba bukatar domin ba da damar karbo bashin, wanda ya ce zai matukar amfanar jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel