Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

  • Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa dalilinsa na komawa jam'iyya mai mulki shi ne ciyar da Najeriya gaba
  • Ya sanar da cewa babu shakka zai yi kokarin janyo gwamnonin jihohi Oyo, Bauchi da Enugu zuwa jam'iyyar mai mulki
  • Tsohon ministan ya ce, ba za a iya ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki ba har sai an zama tsintsiya madaurin ki daya

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya sha alwashin tarkata gwamnonin jihohin Oyo, Bauchi da na Enugu zuwa jam'iyya mai mulki bayan komawarsa a yau.

Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni ne ya gabatar da tsohon ministan ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Fani-Kayode wanda ya zanta da manema labarai, ya ce lokaci yayi da ya dace ya hada kai da shugaban kasa wurin ciyar da Najeriya gaba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Barin wuta ta sama: Gwamnan Yobe ya umurci asibitocin gwamnati da su kula da wadanda suka jikkata

Jerin gwamnonin PDP 3 da Femi Fani-Kayode ya sha alwashin ja zuwa APC
Jerin gwamnonin PDP 3 da Femi Fani-Kayode ya sha alwashin ja zuwa APC. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na ji lokaci ya yi da ya dace in yi abinda ya dace, in saka Najeriya a farko kuma in nuna godiya ta saboda kokarin da aka yi min, ballantana a shekarun nan da suka gabata wurin yaki da rashin tsaro, yakar ta'addanci da 'yan bindiga.
"Ba koda yaushe ba ne ake ba daidai ba, kuma idan lokaci yayi, muna sauya alkibla domin komawa tare da hade kai wurin ciyar da kasar nan gaba.
"Yin hakan ba ya na nufin muna kiyayya da kowa ba ne. Koda a ce muna wata jam'iyyar, za mu iya aiki tare domin cigaban yankuna, kabila da addinanmu," yace.

Ya kara da cewa dole ne Najeriya ta zama tsintsiya madaurin ki daya idan ana so a ceto ta daga wadanda suka sha alwashin durkusar da ita.

Kara karanta wannan

Ba Zan Bada Hakuri Ba Kan Kalaman da Na Yiwa Shugaba Buhari, Gwamna

Kaduna: Kotu ta bukaci malami da ya katse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa

A wani labari na daban, wata kotun shari'a da ke zama a Magajin Gari, Kaduna, a ranar Laraba ta umarci wani malamin makaranta, Yusuf Yusuf da ya datse dukkan wata soyayya da ke tsakaninsa da dalibarsa mai suna Zainab Muhammad.

Alkali Murtala Nasir, ya umarci malamin da ya biya N8, 500 ga Zainab a matsayin kudin shigar da kara da kuma kudin asibiti da ta biya bayan mugun dukan da yayi mata.

Alkalin ya yanke wannan hukuncin bayan sasancin da su biyun suka yi ba a kotu ba, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel