Aisha Yesufu ta fada murna, dan ta ya kammala digiri a jami'ar Ingila

Aisha Yesufu ta fada murna, dan ta ya kammala digiri a jami'ar Ingila

  • Mace mai kamar maza, Aisha Yesufu ta fada farin ciki yayin da dan cikinta ya kammala digirinsa a Ingila
  • Kamar yadda ta wallafa, ta saka bidiyon da take kwasar rawa cike da farin ciki sannan da godiya ga Allah
  • Ta bayyana yadda aka sanar mata cewa ba zai iya karatu ba, amma sai ga shi ya kammala digirinsa yana shekaru 22

Mai fafutuka Aisha Yesufu ta je kafar sada zaumuntar zamani inda ta wallafa hotunan dan ta na cikinta da ya kammala karatu a jami'ar Turai.

Daily Trust ta ruwaito cewa, mahaifiyar cike da alfahari ta wallafa bidiyon ta inda aka gan ta ta na cashewa da 'ya'yanta.

Ta yi bayanin yadda aka sanar da ita cewa dan ta ba zai iya zuwa jami'a ba, ta kara da nuna tsabar jin dadin ta kan yadda yanzu ya sanya mata farin ciki.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: Mu ilmantar da 'yan Najeriya ko kuma su addabi kasa da manyan kasa

Aisha Yesufu ta fada murna, dan ta ya kammala digiri a jami'ar Ingila
Aisha Yesufu ta fada murna, dan ta ya kammala digiri a jami'ar Ingila. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda ta ce, ya na da shekaru 14 aka kai shi makaranta a Ingila kuma ya kammala digiri yayin da yake shekaru 22, Daily Trust ta ruwaito.

"A yayin da aka sanar da kai cewa dan ka ba zai iya zuwa jami'a ba. A yayin da ka gama saka wa zuciyarka hakurin cewa ba zai samu digiri ba, sai Allah ya ce ba haka ba ne!
"Ya na shekaru 14 muka kai shi makaranta a Ingila, a yau ya na da shekaru 22 ya kammala digiri" tace.

Mai fafutukar ta kasance a kanun labarai tun lokacin da ta fito ta dinga magana kan sace 'yan matan makarantar sakandaren Chibok da aka a yi a jihar Borno a 2014 kuma ta bayyana a gaba yayin zanga-zangar EndSARS.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari: Ba zamu iya kin yafewa 'yan bindiga ba, su ma 'yan Najeriya ne

An ga fuskar Yesufu a cikin dukkan labarai na zanga-zangar EndSARS inda ta bayyana a matsayin gwarzuwar gwagwarmayar.

Kaduna: Kotu ta bukaci malami da ya katse soyayyar da ke tsakaninsa da dalibarsa

A wani labari na daban, wata kotun shari'a da ke zama a Magajin Gari, Kaduna, a ranar Laraba ta umarci wani malamin makaranta, Yusuf Yusuf da ya datse dukkan wata soyayya da ke tsakaninsa da dalibarsa mai suna Zainab Muhammad.

Alkali Murtala Nasir, ya umarci malamin da ya biya N8, 500 ga Zainab a matsayin kudin shigar da kara da kuma kudin asibiti da ta biya bayan mugun dukan da yayi mata.

Alkalin ya yanke wannan hukuncin bayan sasancin da su biyun suka yi ba a kotu ba, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel