Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton

Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton

  • Rundunar sojin sama ta yi magana kan jita-jitan da ta dabaibaye wani jirgin yaki da ya jefa bama -bamai cikin kuskure a wani kauye a jihar Yobe
  • Mai magana da yawun rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya musanta cewa rundunar ce ke da alhakin faruwar lamarin
  • Gabkwet ya bayyana cewa aikin NAF na karshe a jihar Yobe bai kasance a karamar hukumar Yunusari ba

Yobe - An yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa wani jirgin sama mallakar rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya kashe mazauna wani gari a jihar Yobe.

Legit.ng ta tattaro cewa mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya yi wannan karin haske a cikin wani rubutu da aka yada a shafin Facebook na Aso Rock Villa a ranar Laraba, 15 ga Satumba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Wani jirgin yaki ya yi luguden wuta a Yobe ya kashe fararen hula da dama

Jirgin yaki ya yi luguden wuta kan al’umman gari? Rundunar soji ta yi martani kan rahoton
Rundunar soji ta yi martani kan rahoton luguden wuta kan fararen hula a Yobe Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ions Intelligence, wata kungiyar tsaro ta yi zargin cewa jiragen yakin NAF yayin da suke aikin yaki da Boko Haram da ISWAP sun jefa bana-bamai bisa kuskure a Kauyen Buhari da ke karamar hukumar Yunusari wanda ya kashe mazauna yankin da dama tare da jikkata wasu.

Gabkwet ya ce rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta karya ne, ya kara da cewa aikin karshe da rundunar NAF ta yi a Yobe ya gudana ne a ranar Lahadi 5 ga watan Satumba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi bayanin cewa aikin na makamai ne kuma ba a yi amfani da bam ko makami mai linzami ba.

'Yan ta'addan Boko Haram sun koma dajin Kaduna – DSS ta ankarar da sauran hukumomi

A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta nemi hukumomin tsaro a Kaduna da su kasance cikin shirin ko ta kwana kan yiwuwar kai hare-hare, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Ta bayyana cewa shugabanni da dakarun kungiyar ‘yan ta'adda na Boko Haram sun koma wani daji a Kudancin Kaduna daga Dajin Sambisa.

A cikin wata sanarwa da jaridar Peoples Gazette ta gani, an ce yan ta’addan sun kaura daga dajin Sambisa a jihar Borno zuwa dajin Rijana da ke karamar hukumar Chikun ta Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel