‘Yan bindiga sun ce tsohuwa tukuf mai shekara 86 ta biya N20m kafin a fito da 'Danta da Jikoki 3

‘Yan bindiga sun ce tsohuwa tukuf mai shekara 86 ta biya N20m kafin a fito da 'Danta da Jikoki 3

  • ‘Yan bindiga sun dauke wani Fasto da Iyalinsa a wani kauye a Zangon-Kataf
  • Rahotanni sun ce an nemi mahaifiyar wannan Fasto ta kawo Naira miliyan 20
  • Juliana Umoh ta roki mutane su taimaka mata da kudi domin a ceto ‘ya‘yanta

Kaduna - Kwanakin baya ‘yan bindiga suka dauke Rabaren Father Luka Yakusak mai limanci a babban cocin katolika na St. Mathew a Zangon-Kataf.

Jaridar Punch tace ‘yan bindigan da suka dauke faston sun bukaci mahaifiyarsa ta biya Naira miliyan 20 kafin a fito da shi da iyalinsa da aka dauka.

‘Yan bindigan sun nemi mahaifiyar malamin cocin mai shekara 86 da haihuwa, Juliana Umoh ta kawo kudi kafin a saki ‘danta, surukarta da jikokinta uku.

Rahoton yace da ‘yan bindigan suka shigo kauyen Anchunna a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, 2021, da karfe 8:00 na dare, ba su taba tsohuwar ba.

Kara karanta wannan

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da magidanci da iyalinsa 4 a Kaduna sun nemi a biya naira miliyan 20

Za su kashe 'da na, matarsa da jikoki 3

Juliana Umoh tace ‘yan bindigan suna mata barazanar za su kashe wadanda ke hannunsu idan ba a iya kawo masu kudin da suka bukata, Naira miliyan 20.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umoh tace ‘dan ta Peter Andrew mai shekara 41 shi ne mai daukar dawainiyar gidan. Tsohuwar tayi kira ga mutane su taimaka a fito mata da ‘ya ‘yan na ta.

Da take magana, wannan tsohuwa tace jikokinta 'yan shekara 12 da 11 ne rak a Duniya, ‘dan autan na su kuma duka-duka bai wuce watanni shida da haihuwa ba.

‘Yan bindiga
Jami'an tsaro a Kaduna Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Ina rokon mutanen Najeriya da sunan Allah, su taimaka, don Allah su taimaka mani da duk abin da za su iya bani domin in ceto ‘ya ‘ya da jikokina.”

Umoh take cewa tun da take a Duniya, ba ta taba ganin Naira miliyan daya ko ta taba ba, har kuma ace ana neman Naira miliyan a matsayin kudin fansa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bindige soja har lahira yayin da suka sace mata da yaranta 2 a Zaria

Wani mazaunin garin Zangon-Kataf ya koka game da abubuwan da ke faru wa, yace a ‘yan kwanakin nan garkuwa da mutanen yana daukar wani salon.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 12 a harin Zangon Kataf. Ba wannan ne karon farko da aka hallaka mutane a yankin na kudancin jihar ba.

Idan za a tuna, Kwamishinan harkoki da tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel