Sojoji sun damke tsohon soja yana jigilar tulin wiwi da kwayoyi daga Ondo zuwa Jihohin Arewa

Sojoji sun damke tsohon soja yana jigilar tulin wiwi da kwayoyi daga Ondo zuwa Jihohin Arewa

  • Sojoji sun kama wasu mutane za su kai kwayoyi daga Ondo zuwa Adamawa
  • Rundunar Operation SAFE HEAVEN tace ta kama har da wani tsohon kurtu
  • An kama wadannan mutane tare da kwayoyi a mota a iyakar Kaduna da Jos

Kaduna - Jim kadan da kama wani tsohon ‘dan sanda da wani mutumi dauke da ganyen tabar wiwi na N9.5m, sojoji sun sake ram da wasu da kwayoyi.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa dakarun Operation SAFE HEAVEN, OpSH sun kama wani mutumi da ake zargin yana dauke da kwayoyi na N7.5m.

Kamar yadda aka kama wancan tsohon ‘dan sanda, rahoton yace shi ma an damke wannan mutum dauke da kwayoyi a boye cikin motar Toyota Camry.

Sojoji sun tare wannan mota mai lambar Legas; KJA 150 EG yayin da suke bincike a kan hanyar Manchok zuwa Jos a karamar hukumar Kaura, Kaduna.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

Jami’in yada labarai na sojoji da ke garin Jos, Manjo Ishaku Takwa yace Operation SAFE HEAVEN sun yi kamu a ranar Talata, 14 ga watan Satumba, 2021.

Manjo Ishaku Takwa a madadin shugaban rundunar, OSH, Janar Ibrahim Ali yace ana zargin darajar tabar wiwin da aka karbe za ta kai Naira miliyan 7.5.

Yana jigilar wiwi
Wani mutumi dauke da ganyen wiwi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jawabin dakarun OSH

“Wadanda dakaru suka kama su ne; tsohon kofur na soja, Essien Friday mai shekara 60 da wani Ibrahim Ali mai shekara 50 a lokacin da aka tare motoci ana bincike a titin Manchok – Jos, Kaura, jihar Kaduna.
“Wadanda aka kama suna ikirarin an ba su aikin dakon miyagun kwayoyin ne daga Ondo zuwa garin Yola, jihar Adamawa."
“Abubuwan da aka karbe sun hada da raf 18 na tabar wiwi da aka mola, wayoyin salula biyu, jakunkunan daukar guzuri uku, abin kyasta wuta, da alabe dauke da N570.”

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sake kashe mutane 12, sun raunata wasu Bayin Allah a Kaduna

“An damka wadanda ake zargi da laifi ga hukumar NDLEA mai yaki da fataucin miyagun kwayoyi domin su gudanar da bincike na musamman.”

Matsalar wutar lantarki

Jiya Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, ya gana da Jakadan Masar, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari yana so matsalar wuta ta zama tarihi.

Daga shigansa ofis, sabon Ministan ya yi zama Jakadan Masar a Najeriya, inda suka yi magana a kan yiwuwar kasashen Afrikan su hada-kai, su taimaki juna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel