Faɗawa Shugaba Gaskiya Yanzun Ya Zama Sabon Matsalar Tsaro a Najeriya, Malamin Addini Ya Magantu

Faɗawa Shugaba Gaskiya Yanzun Ya Zama Sabon Matsalar Tsaro a Najeriya, Malamin Addini Ya Magantu

  • Malamin addinin kirista, Bishop Ransom Bala, yace faɗin gaskiya a wannan gwamnatin ya zama matsalar tsaro
  • Bala yace da zaran ka faɗi gaskiya kan wannan gwamnatin, to daga nan za'a fara bibiyarka, rayuwarka ta shiga matsala
  • A cewarsa akwai bara gurbi a zagaye da shugaban ƙasa, waɗanda ke kokarin boye masa halin da kasa ke ciki

Abuja - Shugaban kiristoci yan Calvary Life na ƙasa da kasa, Bishof Ransom Bello, ranar Talata, ya bayyana cewa yanzun faɗawa shugabanni gaskiya ya zama wani sabon matsalar tsaro, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Yace a halin da ƙasa ke cike yanzun idan aka cire ayyukan yan bindiga, satar mutane, da kuma fashi da makami, sabuwar matsalar tsaron da ta ɓullo itace faɗawa masu rike da madafun iko gaskiya.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Ya Dace Yan Najeriya Su Ɗauka Kan Shugabannin da Suka Gaza Cika Alƙawari, Tsohon Ministan Sadarwa

Bishop Ransom Bello
Faɗawa Shugaba Gaskiya Yanzun Ya Zama Sabon Matsalar Tsaro a Najeriya, Malamin Addini Ya Magantu Hoto: soulmp3.com
Asali: UGC

Jagoran yace:

"Mun samu sabon kalubalen tsaro a Najeriya, idan ka faɗa musu gaskiya, zasu fara yi maka bita da kulli, kuma hakan bai dace ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk wata gwamnati da take son yin abinda ya dace, to wajibi ta saurari mutane kuma ta ɗauki gaskiyar da ake faɗa mata."
"Dan me zan zama cikin tsoro don kawai na faɗawa gwamnati gaskiya kuma sun san cewa gaskiya na faɗa musu? Saboda me rayuwata zata shiga hatsari dan nace gwamnati ta gyara?"
"Kamata ya yi gwamnati ta duba da idon basira kuma ta saurari shawarwari da kuma korafin jama'a."

Shin gwamnati na kama masu faɗin gaskiya?

Bishof Bello ya roki gwamnatin tarayya ta daina kame da kuma cin mutuncin yan Najeriya, waɗanda suka rike gaskiya komai rintsi.

"Muna da damar faɗawa masu rike da mulki da hukumomi gaskiya, matukar sun yi abinda ya dace dole mu yaba."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Shahararren Ɗan Kasuwa Ya Maka Tsohuwar Matarsa a Kotun Musulunci Kan Jaririn da Ta Haifa

"Idan kuma sun kauce wa hanya wajibi mu faɗa musu gaskiya. Amma wannan gwamnatin ta yanzun bata yin abinda ya dace, wannan shine gaskiya."
"Zamu cigaba da faɗin gaskiya saboda akwai bara gurbi a zagaye da shugaban ƙasa, waɗanda suke kokarin ɓoye masa, ya yi tunanin yana kyautatawa yan ƙasa."

A wani labarin kuma Mataimakin Gwamna Ya Yi Magana Kan Shirinsa Na Ficewa Daga Jam'iyyar PDP

Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu, ya bayyana cewa babu wata matsala tsakaninsa da uban gidansa, Gwamna Obaseki.

Shaibu ya faɗi cewa tabbas akwai matsalolin dake faruwa a cikin PDP, amma bai shafi alakarsa da gwamna ba, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel