Sojin Najeriya sun kera motocin da kan iya hango 'yan ta'adda daga nisan tazara

Sojin Najeriya sun kera motocin da kan iya hango 'yan ta'adda daga nisan tazara

  • Rundunar sojin Najeriya ta kirkiro wasu motoci masu hangen nesa don gano 'yan ta'adda
  • Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro suke kara lalacewa a yakuna daban-daban na Najeriya
  • An samar da motocin masu kymarori a jikinsu da kan iya hango abubuwa daga nisan kilomita 6.5

Babban hafsan sojojin kasa (COAS), Laftanar Janar Farouk Yahaya, a ranar Litinin 13 ga watan Satumba, ya ba da sabbin motocin sadarwa na tauraron dan adam wadanda za a tura su ga rundunoni daban-daban na soji a fadin kasar.

Motocin na dauke da kyamarori da kayan aikin lantarki na zamani, kuma rundunar sojan Najeriya ta Cyber ​​Warfare Command, Abuja ta kirkiresu, The Sun ta ruwaito.

Da yake jagorantar COAS yayin ziyarar duba motocin, Kwamandan, Cyber ​​Warfare Command, Birgediya Janar Adamu, ya ce motocin na hango abu daga nisan kilomita 6.5 kuma an sanya masu na'urorin da za su taimaka a hango abubuwa ko da cikin dare ne.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

Sojin Najeriya sun kera motocin da kan iya hango 'yan ta'adda daga nisan tazara
Laftanar Janar Faruk Yahaya, COAS |Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Adamu ya kuma ce motocin na iya jujjuya na digiri 360 kuma suna da irken intanet don baiwa sojoji damar yin kira zuwa cibiyoyin aiki, ofishin COAS, cibiyar yaki ta yanar gizo da kuma sanya ido kan duk ayyukan sojoji a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ci gaba da bayyana cewa motocin, wadanda kuma ke aiki a matsayin cibiyoyi masu iko da sarrafawa, za su ba kwamandoji damar sauke bayanai a wayar su ta hannu da aikawa zuwa ga sauran kwamandojin.

Ba zan lamunci uzirin kowa ba, COAS ya sanar da kwamandojin dakarun soji

Shugaban dakarun sojin kasa, COAS Faruk Yahaya ya ja kunnen cewa ba zai lamunci uziri daga kwamandojin da ke jagorantar dakarun soji ba a filin daga da kuma yakar matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta ba.

Yahaya ya bada wannan jan kunnen a yayin bude wani taro kashi na biyu da na uku na sojin da ke hade a ranar Litinin a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

Ya ce rundunar da ke karkashinsa za ta cigaba da mayar da hankali tare da kokarin ganin ana samun cigaba wurin yakar matsalolin da ake ciki.

COAS ya bayyana cewa ya umarci dukkan sojoji da ke ayyukan samar da zaman lafiya da su cigaba da aikin da suke yi tare da karawa, Daily Nigerian ta wallafa.

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

A wani labarin, Rahotanni sun bayyana cewa an sace wani jigon jam’iyyar PDP kuma jagoran jam’iyyar a gundumar Sanatan Edo ta Kudu, Owere Dickson Imasogie tare da direban sa a safiyar yau.

An sace jigon ne a kan hanyarsa ta zuwa gonarsa lokacin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kama shi da misalin karfe 7 na safe, The Sun ta ruwaito.

Wata majiya kusa da danginsa ta ce:

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

“An yi garkuwa da shi a gonarsa da ke kewayen yankin Obada a karamar hukumar Uhunmwonde. Yana tare da direbansa lokacin da lamarin ya faru."

Asali: Legit.ng

Online view pixel