Kotu ta tsayar da ranar gurfanar da mutane 400 da ake zargi da ɗaukan nauyin ta'addanci a Nigeria

Kotu ta tsayar da ranar gurfanar da mutane 400 da ake zargi da ɗaukan nauyin ta'addanci a Nigeria

  • Za a gurfanar da wadanda ake zargi da daukan nauyin ta'addanci a ranar 17 ga watan Satumba
  • Fadar shugaban kasa ta ce galibin mutanen 400 da ake zargi da daukan nauyin ta'addancin 'yan canji ne
  • Babban lauya mai kare hakkin bil adama, Femi Falana, SAN, ya bukaci Attoni Janar na kasa ya bawa jihohi damar hukunta masu laifin

FCT, Abuja - Wata babban kotun tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar 17 ga watan Satumban 2021 domin gurfanar da mutane 400 da ake zargi da daukan nauyin ta'addanci a Nigeria, Daily Trust ta ruwaito.

Mai shari'a Anwuli Chikere ne zai saurari karar a kotun ta taryya.

Kotu ta tsayar da ranar gurfanar da mutane 400 da ake zargi da ɗaukan nauyin ta'addanci a Nigeria
Za a gurfanar da wadanda ake zargi da daukan nauyin ta'addanci a ranar 17 ga watan Satumba. Hoto: DailyTrust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Fadar shugaban kasa ta sanar a watan Maris cewa ta kama wadanda ake zargin da hannu wurin daukan nauyin ta'addanci ta hanyar taimakawa 'yan Boko Haram samun kudade, galibinsu 'yan canji ne.

Wasu 'yan Nigeria daga Hadadiyar Daular Larabawa ta UAE tare da taimakon 'yan canjin suna tura wa 'yan ta'addan na Boko Haram kudade a cewar rahoton na Daily Trust.

Attoni Janar kuma Ministan Shari'a na Nigeria, Abubakar Malami (SAN) ya sanar da cewa an kammala shiri don gurfanar da wadanda ake zargin wadanda jami'an yan sandan farar hula SSS suka kama su tare da musu tambayoyi.

Falana ya nemi a bawa jihohi damar hukunta masu daukan nauyin ta'addancin

Mutanen kasa sun bayyana damuwarsu kan jinkirin da ake yi kafin fara shari'ar inda lauya mai kare hakkin bil adama, Femi Falana (SAN) ya rubuta wasika ga Malami yana neman a bawa Attoni Janar na jihohi ikon yin shari'a tare da hukunta wadanda aka samu da laifin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

Falana ya nuna damuwarsa kan yadda ba a bawa attoni janar na jihohi ikon hukunta wadanda aka samu da laifukan ta'addanci, fashi da kisa a jihohinsu ba.

Ya ce:

"Irin wannan sakacin na hukuma ne yasa ake samun karuwar hare-haren da yan bindiga ke kaiwa. A lokuta da dama, yan sanda da sauran hukumomin tsaro na kama masu laifin amma a sake su,su koma su cigaba da laifukan."

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

A wani labarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel