Majalisar dattawa ta bayyana burinta kan sabis na 5G, ta ce NCC ta samar da N350bn

Majalisar dattawa ta bayyana burinta kan sabis na 5G, ta ce NCC ta samar da N350bn

  • Majalisar dattawa ta bukaci hukumar NCC ta tabbatar ta samar wa Najeriya makudan kudade ta amfani tsarin 5G
  • Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin tarayya ta amince a fara amfani da tsarin sadarwar 5G a kasar
  • Hukumar NCC ta bayyana irin shirin da ta ke dashi da kuma hasashen da ta ke na samar wa kasa kudaden shiga

Abuja - Majalisar Dattawa ta nemi Hukumar Sadarwa ta Najeriya da ta yi amfani da tsarin sadarwa na 5G don samar wa Gwamnatin Tarayya kudin shiga N350bn a cikin kasafin kudi na shekarar 2022.

Idan baku manta ba, mun ruwaito muku cewa, gwamnatin tarayya ta amince a dasa tare da fara amfani tsarin sadarwar 5G a Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta hana jihar Legas da Rivers karbar kudin harajin VAT

Majalisar dattawa ta bayyana burinta kan sabis na 5G, ta ce NCC ta samar da N350bn
Tsarin sadarwar 5G | Hoto: quinkpost.com
Asali: UGC

Wannan shi ne hukuncin kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da ke aiki kan Tsarin Kudin Matsakaicin Shiri na 2022-2024, lokacin da gudanarwar Hukumar NCC ta bayyana a gaban kwamitin zauren majalisar.

Shugaban kwamitocin hadin gwiwa, Sanata Solomon Adeola, ya ce kasafin kudin 2022 na NCC ba zai zama N115bn ba, wanda shine adadin da ta yi hasashe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Muna ba da shawarar samar da N350bn. Wannan kenan saboda dole ne a sami tsinkayar siyar da tsarin sadarwa bayan kaddamar da hanyar sadarwar 5G.”

Martanin hukumar NCC kan wannan bukata

Manajan Darakta na NCC, Umar Danbatta, yayin da yake kare kasafin kudin hukumarsa a gaban kwamitin Majalisar Dattawa MTEF/FSP ya ce hukumar za ta iya samar da Naira biliyan 400 daga sakin tsarin na 5G.

Danbatta ya ce hukumarsa ta tsara kasafin kudi na N162bn na 2021 amma a farkon kwata na 2021.

Kara karanta wannan

Hukumar ICPC ta kwato garkame kadarori da dan majalisar Yobe ya boye na mazabarsa

Yace:

"Mun wuce adadin saboda mun sami damar samar da N181bn."
"Wannan ya faru ne saboda biyu daga cikin kamfanonin sadarwar mu na wayar salula, MTN da Airtel, sun nemi tsarin kuma hakan ya bamu kudaden shiga da yawa."

A cikin kasafin kudi na shekarar 2022, ya ce:

"Muna hasashen samar da N115bn. Tsinkayar ba ta yi la’akari da gwanjon tsarin 5G ba.”

Shugaban na NCC ya kara cewa:

"Kowane tirke na 5G yana iya farawa akan farashin N75bn. Haka kuma, a lokacin gwanjonsa, zai iya kaiwa har N100bn.

“Farashin gwanjon tsarin, a shekarar 2022 zai baiwa Gwamnatin Tarayya, N300bn. Lokacin da aka kara kudin shiga akansa da aka yi hasashe, muna sa ran samar da sama da N400bn saboda gwanjonsa za a yi."

Daga maganganunsa, hasashe ya nuna NCC za ta iya cimma burin majalisar dattawa na samar da sama N350bn.

An cimma nasara: Minista Pantami ya ce saura kiris 5G ya fara aiki a Najeriya

Kara karanta wannan

NYSC za ta zakulo hazikan mambobin bautar kasa don tsoma su a harkar fina-finai

Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta dasa cibiyar sadarwa ta 5G a cikin kasar don kara gudun cudanyar yanar gizo, in ji TheCable.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Isa Pantami ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

Pantami ya ce shawarar dasa cibiyar sadarwa ta 5G ta biyo bayan sakamakon cikakken bincike, kwakwaf da gwajin kawar shakku kan barazana ga tsaro ko kiwon lafiya.

Pantami, wanda ya ce babban abin da ya fi damun gwamnati shi ne tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan Najeriya wajen amfani da ayyukansu a bangaren sadarwa, ya dora laifin jinkirin da aka samu na dasa cibiyar sadarwa ta 5G kan wasu makiran shakku da ake yadawa.

A cewarsa:

“Gwamnatin mu mai sauraran mutane ce; don haka muna sauraron sukar da ta dace, muna girmama hakan kuma muna yabawa kuma akalla muna kimanta aikatawa.

Kara karanta wannan

Abdurrassheed Bawa: Barayi suna amfani da Bitcoin wajen sace kudi a duniya

"Mun kai kololuwar mataki kan 5G, to, wani batun ya taso cewa 5G yana da alaka da Korona; mutane da yawa ciki har da masu ilimi sun fara yayata batun ba tare da tantancewa ba."

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur

A wani labarin, Rahoton da muke samu daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur.

Legit.ng Hausa ta samo wata sanarwar mai ba shugaba shawari na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, inda ta bayyana rattaba hannun shugaban a yau Litinin 16 ga watan Agusta, 2021.

Femi Adesina ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin dokar masana'antar man fetur na shekarar 2021 don zama doka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel