NEDC ta fara gina makarantu ga talakawa a yankunan da Boko Haram ta addaba

NEDC ta fara gina makarantu ga talakawa a yankunan da Boko Haram ta addaba

  • Hukumar raya yankin Arewa maso gabas (NEDC) ta bayyana kudurin gina makarantu a yankunan Arewa maso gabas
  • Ta bayyana dalilin gina makarantun da cewa, hakan zai habaka ilimi a yankunan da Boko Haram ta lalata
  • Hukumar ta bayyana adadin makarantun da za ta gina a kowane yanki na jihohin Arewa maso gabas

Yobe - Hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) ta fara gina karin makarantu a jihar Yobe, da sauran sassan arewa maso gabas, a matsayin wani mataki na magance karuwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin.

Manajan Daraktan Hukumar, Mohammed Alkali ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Gasua, jihar Yobe, Ripples Nigeria ta ruwaito.

NEDC ta fara gina makarantu ga talakawa a yankunan da Boko Haram ta addaba
Gwamnati za ta gina makarantu a Arewa maso gabas | Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Ya ce rikicin Boko Haram ya lalata makarantun firamare da na sakandare a yankin Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Shugaban sojin sama: Luguden da sojoji ke wa 'yan ta'adda ya na haifar da sakamako mai kyau

Manajan Daraktan ya bayyana cewa:

“Yawaitar talauci hade da rashin tsaro, ya sanya kimanin yara 600,000 sun kasa wuce matakin firamare ko sakandare.
“Don haka, miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta a Yankin har yanzu ba su samu wadataccen ilimi ba, wannan yasa ake da bukatar babban tallafi a ci gaban abubuwan more rayuwa na makaranta.
“A sakamakon haka, Hukumar ta yanke shawarar gina manyan makarantu guda uku ko inganta wadanda ake da su a kowace Jiha ta yankin, 18 kenan, daya a kowace Gundumar Sanata.
"Hakanan zamu ci gaba da habaka tsarin cikin makarantun tare da tallafi mai taushi kamar horar da malamai, manhajar ilimi da ingantayya."

A martaninsa, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda shugaban ma’aikatansa, Abdullahi Yusuf ya wakilta, ya ce aikin NEDC “ya dace kuma abinda ake so”.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

Ya kalubalanci duk masu ruwa da tsaki a yankin da su taimaka su kare ayyukan.

Soji sun damke babban dan Boko Haram, sun kama buhuhunan sinadaran hada Bam 281

Hukumar Sojin Najeriya ta samu nasarar damke kasurgumin dan Boko Haram a Arewa maso gabas kuma ta kai simame ma'ajiyar sinadaran hada bama-bamai a Borno da Yobe.

Diraktan hulda da jama'a na hukumar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a jawabin da ya saki a shafin Facebook.

Yace wannan nasara ya biyo bayan hare-haren da rundunar Operation HADIN KAI (OPHK) suka kai.

Yace:

"Dakarun Sector 2 Joint Task Force na Operation HADIN KAI (OPHK) sun damke wani babban dan Boko Haram kuma sun kai simame ma'ajiyar ajiyan sinadaran hada bama-bamai a Damboa dake jihar Borno; da kuma Gashua dake jihar Yobe."

Barazanar tsaro: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro

Kara karanta wannan

'Yan bindigan Zamfara 'yan ta'adda ne ba 'yan fashi ba, Cewar Akeredolu

A wani labarin, Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da rufe makarantun sakandire na kwana 30 da ke jihar daga cikin kananan makarantu 34 saboda matsalar rashin tsaro.

Rufewar, a cewar wata sanarwa daga kwamishiniyar ilimi , Mrs. Wilbina Jackson, za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Satumba, 2021 har sai an sake samun wani ci gaba.

Sanarwar da wakilin jaridar Punch ta gani ta ce daukar wannan mataki wani yunkuri ne na tabbatar da tsaron dalibai saboda rashin tsaro da ke addabar kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel