Shugaban sojin sama: Luguden da sojoji ke wa 'yan ta'adda ya na haifar da sakamako mai kyau

Shugaban sojin sama: Luguden da sojoji ke wa 'yan ta'adda ya na haifar da sakamako mai kyau

  • Shugaban sojin sama, Oladayo Amao, ya ce ayyukan da sojoji ke yi a yankin arewa maso gabas na kawo sakamakon da ake so
  • Ya ce babu shakka 'yan ta'addan yankin arewa maso gabas suna kwasar kashin su a hannu a wurin dakarun sojin
  • Shugaban ya kara bada tabbacin cewa, zaman lafiya zai dawo kasar nan kuma rashin tsaro zai zama tarihi

Borno - Oladayo Amao, shugaban dakarun sojin sama, ya ce lugude da ayyukan sojoji kan 'yan ta'adda ya na bada sakamako mai kyau.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, takardar da Edward Gabkwet, mai magana da yawun NAF ya fitar, Amao ya sanar da hakan ne yayin da ya kai ziyara ga dakarun da ke Maiduguri na da Yola.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Da yawan shanun da ake sacewa a Arewa 'yan Kudu ake sayarwa

Shugaban sojin sama: Luguden da sojoji ke wa 'yan ta'adda ya na haifar da sakamako mai kyau
Shugaban sojin sama: Luguden da sojoji ke wa 'yan ta'adda ya na haifar da sakamako mai kyau. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Dakarun suna daga cikin jami'an operation Hadin Kai, tsohuwar rundunar operation Lafiya Dole.

A yayin ziyarar, Amao ya samu bayani daga Nnamdi Ananaba inda ya bada takaitaccen bayani kan manyan nasarorin da sojin saman suka samu wurin dakile ta'addanci a jihar Borno, balle a kwanaki talatin da suka gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin jawabinsa, shugaban dakarun sojin ya jinjinawa dakarun kan yadda suka mayar da hankali wurin shawo kan matsalar ta'addanci a arewa maso gabas.

Ya yi kira gare su da su cigaba da aikin da suka saka gaba, inda ya kara da cewa sakamakon da ake samu ya na da kyau, TheCable ta ruwaito.

Shugaban sojin saman ya bayyana tabbacinsa kan cewa kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta ya kusa zama labari.

Ya ce NAF ta na aiki tukuru da sauran hukumomin tsaro wurin ganin bayan dukkan ta'addanci da kuma samar da zaman lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Ba mu sukar matakan tsaro da gwamnati ta dauka, Dattawan Arewa

Amao ya mika godiyarsa ga jami'an kan yadda suka jajirce tare da sadaukar da kan su zuwa aikin tsaron kasa.

NAPTIP: Rashin jituwa da Minista Sadiya Faruk ya sa aka fatattaki tsohon sanata

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami Sanata Basheer Mohammed, darakta janar na hukumar yaki da safarar jama'a (NAPTIP). Daily Trust ta ruwaito cewa, an sallami Mohammed kasa da watanni hudu da ya karbi ragamar hukumar.

A wata takarda ta ranar Laraba, babban mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya ce shugaban kasan ya amince da nadin Fatima Waziri-Azi a madadin Mohammed.

Shehu ya ce an yi nadin ne sakamakon bukatar ministan walwala da jin kan 'yan kasa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel