Za a nadawa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan sarautar Iyin Ekiti

Za a nadawa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan sarautar Iyin Ekiti

  • Za a nadawa Ahmad Lawan sarautar Iyin-Ekiti, a karamar hukumar Irepodun/Ifelodun
  • An bayar da rahoton cewa za a nada masa masarautar ne bisa ga irin gudummuwar da ya bayar wajen ci gaban ƙasa gaba ɗaya
  • Sauran wadanda kuma za a karrama su ne: Manjo Janar Bamidele Olawumi da matarsa, Ba'isra'ile, Him Hille da matarsa, da sauransu

Ekiti - Za a nadawa Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, da wasu fitattun 'yan Najeriya shida sarautar Iyin-Ekiti, a karamar hukumar Irepodun/Ifelodun ta jihar Ekiti.

Sauran su ne tsohon Darakta Janar na Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), Manjo Janar Bamidele Olawumi da matarsa, Ba’isra’ile, Him Hille da matarsa, Mista Ayodeji Adeosun da Mrs Veronica Ndanusa.

Za a nadawa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan sarautar Iyin Ekiti
Za a nadawa shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan sarautar Iyin Ekiti Hoto: The Guardian
Asali: Twitter

Sarkin Iyin-Ekiti, Oba Adeola Ajakaiye; Oluyin na Iyin-Ekiti, ya bayyana hakan a ranar Juma'a a wani taron manema labarai a Iyin-Ekiti, jaridar PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

NYSC za ta zakulo hazikan mambobin bautar kasa don tsoma su a harkar fina-finai

Rahoton ya kuma kawo cewa za a shafe mako guda don gudanar da taron cika shekara guda da hawan sarkin kan karagar mulki daga ranar Litinin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ajakaiye ya ce za a yi masu nadin sarautar ne don karrama gudummawar da suka bayar wajen ci gaban al'umma da kasa baki daya.

A cewar basaraken, sauran ayyukan da aka shirya don tunawa da ranar sun hada da, kaddamar da Naira miliyan 500 na asusun raya masarauta da duba lafiya.

Sauran ayyukan sun hada da warkar da mutane da yi masu tiyata da gasar kwallon kafa, da sauransu.

Ya yi kira ga ‘ya’yan garin maza da mata, na gida da na kasashen waje, da su rika bayar da gudunmawarsu a ko da yaushe don ci gaban al’umma.

Sakataren masarautar Oluyin, Cif Opeyemi Arije, ya lura cewa garin ya sami gagarumin zaman lafiya da ci gaba a cikin shekara guda na mulkin sabon sarkin.

Kara karanta wannan

VAT: Shari’ar Gwamnatin Ribas da Gwamnatin Tarayya ya raba kan Jihohi zuwa gidaje 3

Arije, wanda ya ninka a matsayin Sakataren Kwamitin Shirye -shirye na Karamar Hukumar, ya ce al'umman suna fuskantar wani sabon ci gaba.

“Sarkin mu ya yi gyaran fuska ga fadar ta hanyar samar da ofishi ga Oluyin a Majalisa da karamin dakin taro.
“Oba Ajakaiye ya kuma yi murna da ƙaddamar da rijiyoyin burtsatse guda biyar waɗanda yan asalin yankin suka ba da gudummawa, ya tallafa wajen ƙirƙirar LCDA da hedikwatarsa ​​a Iyin-Ekiti tare da samar da kayan sakatariyarsa."

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani tsohon sarki a jihar Anambra, Alex Edozieuno, da direbansa, wanda aka bayyana sunansa da Chukwuemeka a ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an yi musu kwanton bauna inda aka kashe su a Otuocha da ke karamar hukumar Anambra ta gabas a jihar da sanyin safiyar Juma’a.

Kara karanta wannan

Jami'ar Nigeria ta fatattaki Lakcara mai koyar da turanci saboda baɗala

Edozieuno yana daga cikin sarakunan gargajiya 12 da gwamnatin jihar Anambra ta sauke kan zuwa Abuja tare da wani Prince Arthur Eze, don ganin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ba tare da izinin gwamnati ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel