Gyadar doguwa: Yadda ya tsira daga hannun Miyagun da suka yi garkuwa da shi - Gumi

Gyadar doguwa: Yadda ya tsira daga hannun Miyagun da suka yi garkuwa da shi - Gumi

  • Wani Injiniya da ‘Yan bindiga suka nemi su dauke a garin Kaduna ya tsere
  • Mutumin ya sha da kyar ne bayan ‘Yan bindiga sun shiga inda ba su sani ba
  • Ahmad Gumi yace wannan mutumi ya bi ta cikin gonar masara ne ya sulale

Kaduna - Wani mutumi da ya tsira daga hannun ‘yan bindiga ya bada labarin halin da ya samu kan shi. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoton.

Babban malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi shi ne ya kawo labarin kubutar da wannan Injiniya daga cikin jeji.

Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya kawo wannan labari a lokacin da yake maida wa mai magana da bakin shugaban kasa, Femi Adesina martani.

Kara karanta wannan

Kai Ɗan Kanzagi Ne, Muƙunshin Gishiri Ka Fi Gishiri Zaƙi, Gumi Ya Yi Wa Kakakin Buhari Wankin Babban Bargo

Da yake magana a Kaduna, jaridar tace shehin ya kawo kissar abin da ya faru da wani mutumi da aka yi garkuwa da shi, amma Allah ya yi, ya kubuta.

“Jiya wasu mutane biyu da abin ya shafa suka zo mani, suka ce ‘yan bindiga sun dauke ‘yanuwansu a kewayen Kaduna - Rigachukun da Keke.”

An yi garkuwa da shi
Wani kungurmin jeji Hoto: theconversation.com
Asali: UGC

“Wani wanda ya tsere daga Keke yace da ya fahimci ‘yan bindigan baki ne a jejin, ya ji suna tuntubar ‘yan gari domin su nuna masu hanya.”
“Daga nan sai ya samu kwarin gwiwar tsere wa.”

Wannan mutum da yake yana da sauran kwana a gaba, ya bi ta cikin shukokin masara ya sulale.

A halin yanzu gonaki sun ciko da kayan amfanin gona, hakan ya ba wannan Injiniya dama ya ratsa ta cikin masarar da ta fito, ya tsere ba tare da an lura ba.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga suna sulalewa zuwa makwabta yayin da Sojoji suka rutsa Zamfara da ruwan wuta

Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya kawo wannan labarin ne domin ya nuna cewa luguden wuta da ake yi wa ‘yan bindiga a Zamfara ba zai zama mafita ba.

"Idan aka rutsa Zamfara, za su koma wasu wuraren. To za a ce za a rufe hanyoyin sadarwa a ko ina a Najeriya ne?

Tarihin rikicin Zamfara

Wani Masani da ya dade yana binciken rikicin Zamfara ya gabatar da takarda da aka yi wa taken I am Bandits, inda ya fede lamarin rashin tsaro a jihar Zamfara.

Dr. Murtala A. Rufa’i wanda ya yi shekara da shekaru yana nazarin wannan lamarin yace akwai hannun 'yan siyasa, sarakunan gargajiya da kuma jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel