Kungiyar Oyo ta gargadi sarakunan gargajiya, tana so a binciki ziyarar da Gumi ya kai jihar

Kungiyar Oyo ta gargadi sarakunan gargajiya, tana so a binciki ziyarar da Gumi ya kai jihar

  • Wata kungiya mai suna Alliance for Oke-Ogun Development ta nemi hukumar DSS da ta binciki dalilin ziyarar da Sheikh Gumi ya kai jihar
  • Ta yi zargin cewa ziyarar Shehin Malamin wani yunkuri ne na mayar da yankin na Fulani
  • A makon nan ne Gumi ya ziyarci garin Igboho, mahaifar mai fafutukar kasar Yarbawa, Sunday Igboho

Oyo - Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Alliance for Oke-Ogun Development, a yankin Oke-Ogun na jihar Oyo, ta yi kira ga hukumar DSS da ta binciki dalilin ziyarar da Sheikh Ahmad Gumi ya kai garin Igboho.

Mai fafutukar Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho dan asalin garin Igboho ne, hedkwatar karamar hukumar Oorelope ta jihar Oyo.

Kungiyar Oyo ta gargadi sarakunan gargajiya, tana so a binciki ziyarar da Gumi ya kai jihar
Kungiyar Oyo ta gargadi sarakunan gargajiya, tana so a binciki ziyarar da Gumi ya kai jihar
Asali: Facebook

Jagoran kungiyar ta AOD na kasa, Cif Abiodun Fasasi, a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis ya yi zargin cewa ziyarar Gumi wani yunƙuri ne na mayar da yankin Oke-Ogun na Fulani.

Kara karanta wannan

Ziyarar Da Sheikh Gumi Ya Kai Garin Igboho 'Neman Rigima' Ne, In Ji Basarekan Yarbawa, Gani Adams

Kungiyar OAD ta yi ikirarin cewa 'yan ta'adda na tserewa daga Arewa maso Gabas bayan nasarar da Sojojin Najeriya suka samu a kan su, jaridar Punch ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ta yi kira ga sarakunan gargajiya a yankin da su yi taka tsantsan da yan cikin gida wadanda, a cewarsu a shirye suke su mika kai ga 'yan ta'adda bori ya hau.

Ta kara da cewa:

”Abin da ya fi tayar da hankali shine cewa wani dan Oke Ogun na iya karbar bakuncin mutum kamar Gumi, muna son DSS ta binciki ainihin dalilin ziyarar tasa; dole ne a binciki wanda ya sauke shi. Mutumin shi ne wanda aka dora wa alhakin jagorantar kira ga yiwa 'yan bindigar afuwa."
“Babban kungiyar zamantakewa ta Oke Ogun, Alliance For Oke Ogun Development, suna amfani da wannan damar don kira ga Gwamnatin Tarayya, Babban Jami’in Tsaro na Jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde, don duba wannan lamari.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun far ma matafiya, sun yi garkuwa da mutum 5 a Ondo

"Muna kuma kira ga sarakunan gargajiyar mu da daukacin jama'ar jihar da su kasance cikin shirin ko -ta -kwana kan bakin da ka iya haifar da hadari ga lafiyarmu."

Sai dai jaridar ta ce a lokacin da aka tuntubi Gumi, a kashe lambobin wayarsa suke kuma bai amsa sakon tes da aka aika wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Rashin tsaro: Bidiyo ya bayyana yayin da Sheikh Gumi ya ziyarci mahaifar Sunday Igboho

A baya mun kawo cewa Sheikh Ahmad Gumi, malamin addinin Islama na jihar Kaduna, ya ziyarci garin Igboho da ke jihar Oyo, garin mai fafutukar kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

Legit.ng ta rahoto cewa an ga Gumi a garin Igboho tare da tsohon babban jami'in hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf.

An ga Gumi da Yusuf tsaye a gaban allon makarantar Muslim Grammar a Modeke-Igboho a wani faifan bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel